Manyan abubuwa guda 8 dake kawo mutuwar aure daga bangaren Miji

Manyan abubuwa guda 8 dake kawo mutuwar aure daga bangaren Miji

Sanannen abu ne cewar mutuwar aure ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma Musulmai, musamman a yankin Arewa kasar Hausa, inda abu ne mai wuya ka ga wani mutumi, namiji ko mace da babu matsalar mutuwar aure a gidansu.

Da wannan dalili ne Legit.ng ta kawo muku jerin abubuwa guda Takwas da suke yin dalilin mutuwar aure cikn sauki ko kuma samar da rashin zaman lafiya a tsakankanin ma’aurata, wadannan kalulabe sun hada da;

KU KARANTA: Siyasar Kano: Kwamishinan Ganduje ya dauki alwashin tika Kwankwaso da kasa

KARYA:

Sau dayawa ana samun Maza dake yiwa Matan da zasu aura karya, ma’ana su nuna masu cewa sun mallaki wani abun duniya, alhali su kansu sun san karya ne, amma dayake su kuma Mata da kwadayi garesu, sai su yarda, sai bayan anyi aure, sai ta fahimci ashe duk karya ce, daga sai rikici ya barke, wanda ka iya kawo mutuwar auren.

RASHIN KULAWA

Wani mummunan dabi’a da aka san Mazan Hausa Fulani itace ta rashin kulawa da Matansu, wanda ita kuma mace babu abinda takeso samada kulawa, idan har ya zama baka iya kulawa da bukatar matarka kamar abinda ya shafi abinci, sutura da dukkanin sauran bukatunta, to dole zasu sami matsala da mijinta wanda zai iya kawo rabuwarsu.

RASHIN TSAFTA:

Cikakkiyar Mace na so taga Mijinta ya nada tsafta da kuma kula da jikinshi, kamar yadda shima Miji ke son ganin Matarsa cikin tsafta, ado da kwalliya, don haka idan ya zamana, Matarka mai tsafta ce, kai kuma aka sameka da akasin haka, tabbas za’a samu matsala a irin wannan zamantakewa, haka zalika akwai irin mazan da kwalliyarsu na zuwa wajen aiki ne ko kuma kasuwa, banda Matansu.

CIN AMANA:

Dayawa daga cikin Maza suna cin amanar matansu ta hanyar neman matan banza, a maimakon su kara aure, wanda wasu lokutan sai ka samu cewa mace ta kama mijinta da matar banza ko a cikin gidanta ko kuma a waje wanda wannan yana kawo rabuwar aure.

ZARGI:

Maza dayawa sukan yi zargin matansu akan abinda ya zamanto su matan basa aikatawa, kamar neman maza, sata, ko makamancin haka wanda wannan shima yana raba aure sosai.

MATSALAR IYAYE:

Wasu iyaye, musamman iyaye Mata suna da son nuna akan yayansu har bayan sun yi aure, wanda hakan zai ga an fara samun gasa da kishi a tsakanin Uwar Miji, da Matarsa, ko kuma Uwar Miji da Uwar Mata, wanda hakan na kazanta har ya kai ya samar da rashin jituwa a tsakanin ma’auratan.

MATSALAR YAN’UWA

Kamar yadda aka tattauna batun Iyaye, su ma yan’uwa, musamman na bangaren Miji suna taka rawa wajen mutuwar aure, sai ka ga wasu suna matsa ma Matar dan uwansu babu gaira babu dalili, sharri da nuna mata kiyayya, wanda hakan sai ya kai ga ta fara jin haushin Mijinta, daga nan sai aure ya fara tangal tangal.

MATSALAR ABOKAI

Kamar yadda maganar take, ‘Nuna min abokinka, zan fadi irin halayyarka’, haka abin yake har a lamarin aure, don kuwa idan mutum ya yi dace da abokan kirki, tabbas zai samu shawarwari masu inganci daga garesu dangane da rayuwar aure, idan kuma aka samu akasin haka, toh fa matsala ta samu, don kuwa daga zugi sai shawarin banza dai dinga samu daga garesu, dangane da matarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: