Shugabancin Igbo a 2023 zai kawo karshen ayyukan IPOB – Kungiyar Ohanaeze
Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo ta babbatar ma yan Najeriya cewa ayyukan kungiyar masu fafutukar neman yan Biyafara wanda aka fi sani da IPOB zai zo karashe ne idan kasar ta tsayar da dan Igbo a matsayin shugaban kasa a 2023.
Yayin da yake jawabi a wani ako da ya aika wa jaridar Vanguard, Shugaban kungiyar, Mazi okechukwu isiguzoro ya bayyana cewa shugabancin Igbo a 2023, zai sa Kabilar Igbo farin ciki sannan kuma ayyukan kungiyar IPOB zai zo karshe.
Ya bayyana cewa sauran yankuna sun yasar da yankin kudu maso gabas da dadewa kuma bisa wannan dalilin ne yasa yankin take neman a taushe ta.
Yace: "Shugabancin dan Igbo a 2023 da kasancewar dan Arewa a matsayin mataimakin shugaban kasa, zai kawo karshe ga ayyukan IPOB. Yan Igbo zasu gabatar da daya daga cikin gwamnonin yankin kudu maso gabas a matsayin wanda ya fi cancanta ya maye gurbin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
K KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu za ta saurari karar da IMN ta shigar na kalubantar haramta ayyukanta da aka yi a watan Satumba
“Don haka mun amince da shugabancin Gwamnonin yankin kudu maso gabas karkashin jagorancin Gwamna Umahi, tare da basu tabbacin samun aminci da kuma goyon baya daga garemu.
“Zamu yi iya abunda zamu iya don kare su daga duk wani tursasawa ko ci da ceto daga kowace kungiya.”
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng