Ibo ne manyan masu hannun jari a Najeriya, ba za mu fice ba - In ji Iwuanyanwu

Ibo ne manyan masu hannun jari a Najeriya, ba za mu fice ba - In ji Iwuanyanwu

  • Gogaggen dan siyasa kuma mawallafi, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, ya ce wadanda ke fushin Ibo su bar Najeriya suna bata lokacin su ne
  • A cewar dan siyasar haifaffen Imo, Igbo ba za su iya barin Najeriya ba saboda su ne manyan masu ruwa da tsaki a kasar
  • Iwuanyanwu ya kuma bayyana cewa zai zama bala’i ga yankin da kuma Nahiyar Afirka idan Najeriya ta rabu

Shahararren dan siyasar nan na kudu maso gabas, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, ya bukaci masu rajin ballewar Najeriya da su janye takobin su, yana mai cewa zai zama bala’i ga ‘yan Najeriya da ma dukkan yan Afirka idan Najeriya ta wargaje.

Iwuanyanwu, wanda ya kasance memba na kwamitin amintattu na jam'iyyar Peoples Democratic Party ya bayyana hakan a lokacin da yake saka hannun jari a matsayin babban mai kula da Wasannin Kwallon Kasa daga Kungiyar Raya Wasanni a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ba zan taba ziyartar Shugaba Buhari a Aso Rock ba, Gwamnan Najeriya

Ibo ne manyan masu hannun jari a Najeriya, ba za mu fice ba - In ji Iwuanyanwu
Iwuanyanwu ya ce kabilar Ibo ne manyan masu hannun jari a Najeriya Hoto: Stefano Montesi-Corbis
Asali: Getty Images

'Yan Igbo suna sha'awar tsarkake Najeriya

Ya ce 'yan kabilar Ibo sune manyan masu hannun jari a Najeriya kuma wadanda ke fafutukar ballewar kabilar daga kasar suna aikata babban kuskure.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, na shirin kayyade karin kayayyakin kasashen waje a dokar shigo da kaya

Jaridar Leadership ta nakalto shi yana cewa:

“Abu ne mai raɗaɗi a gare ni cewa a wannan matakin na rayuwata, Najeriya ta kusan kaiwa ga wargajewa kuma zai zama bala’i ga yan Najeriya da yan Afirka idan mutane suka bar ƙasar nan ta wargaje. Kada muyi kuskure game dashi.
“Akwai wasu mutane da ke cewa a kyale Igbo, wannan babban kuskure ne suke yi. Babu inda Ibo za su je. Idan Najeriya kasa ce ta kamfanoni, Ibo ne manyan masu hannun jari, suna saka hannun jari a ko'ina kuma ba za ku iya fatattakarsu ba.
“Igbo ba zai iya tafiya ba, wannan ita ce gaskiyar magana. Ko da wasu suna son tafiya, Igbo za su ci gaba da kasancewa saboda a bangaren saka jari su ne manyan masu hannun jari.”

A bar yan kabilar igbo idan ballewa suke so, ba za mu iya wani yaki ba: Dattawan Arewa

A wani labarin kuma, kungiyoyin 'yan asalin yankin Biafra (IPOB) da kungiyar fafutukar tabbatar da kasar Biyafara mai mulkin mallaka (MASSOB) suna yakin neman rabewar yankin kudu maso gabas daga Najeriya.

Nnamdi Kanu ne ya kirkiri kungiyar IPOB a shekarar 2012, yayin da RSh Ralph Uwazuruike ya kafa kungiyar MASSOB a shekarar 1999.

Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da aka yi a Abuja a ranar Litinin, Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar, ya ce hargitsin da Ibo ke yi na ballewa ya fara yin yawa, yakara da cewa shugabannin kasar sun nuna goyon bayan wannan shawarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng