Da dumi-dumi: Igbo sun fitar da mutane 11 da suke so su fito takarar shugabancin kasa

Da dumi-dumi: Igbo sun fitar da mutane 11 da suke so su fito takarar shugabancin kasa

- An ware 'yan siyasa 11 daga yankin Kudu maso yamma a matsayin wadanda kabilar Igbo ke sa rai za su fito takarar shugabancin kasa a 2023

- Kungiyar da ta fitar da sunayen 'yan siyasar tace za ta ware ainahin dan takarar ta a zagaye na karshe wajen zabe

Kungiyar dake goyon bayan Igbo suyi shugabancin kasa ta (IPSC), ta ware mutane 11 daga yankin Kudu maso Yamma da ake sa ran zasu fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.

A wata ganawa da kungiyar tayi da manema labarai a jiya Alhamis 27 ga watan Agusta, a Abuja, ta ce za a daina kokarin kafa yankin Biafra idan Najeriya ta fitar da shugaban kasa daga yankin Igbo a shekarar 2023.

Da dumi-dumi: Igbo sun fitar da mutane 11 da suke so su fito takarar shugabancin kasa
Da dumi-dumi: Igbo sun fitar da mutane 11 da suke so su fito takarar shugabancin kasa
Asali: UGC

A cewar Vanguard, shugaban kungiyar ta IPSC, Olukayode Oshinariyo, yace sun ware mutane 11 dinne bayan kwakkwaran nazari.

Ya ce kungiyar tayi nazari akan iliminsu, kwarewa, lafiya, da kuma shekaru kafin ta ware sunayen su.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Jigon jam'iyyar APC da mutum sama da 3,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo

Sunayen da kungiyar ta fitar sun hada da:

1. Peter Obi

2. Ogbonnaya Onu

3. Chris Ngige

4. Sanata Rochas Okorochas

5. Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi

6. Sanata Orji Uzor Kalu

7. Ike Ekweremadu

8. Eyinnaya Abaribe

9. Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi O

10. Sanata Ifeanyi Uba

11. Farfesa Kingsley Moghalu

Shugaban kungiyar ya ce za su gabatar da shawarwari da bincike akan wadannan mutane 11 da suka ware daga yankin na Kudu maso Yamma.

Ya ce kungiyar za ta ware dan takararta bayan gama zaben a cikinsu.

Kungiyar ta bukaci mutanen yankin Kudu maso Yamma dasu rungumi zaman lafiya da hadin kai domin ganin cewa Igbo ya shugabanci Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel