Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

  • Wata kungiyar kabilar Ibo ta bayyana bukatar ta ga gwamnatin Burtaniya kan kame Nnamdi Kanu
  • Ta ce Kanu dan kasar Burtaniya ne, don haka su san yadda za su yi su kare hakkinsa daga hannun Najeriya
  • Ta kuma bayyana cewa, kama shi da aka yi ba bisa ka'ida bane tare da bayyana hujjojinta na fadin haka

Kungiyar 'World Igbo Congress' ta bukaci Gwamnatin Burtaniya da ta kare hakkokin jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, bayan kamun da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi masa.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa Kanu dan kasar Birtaniyya ne, don haka, ya kamata gwamnatin Burtaniya ta kiyaye masa hakkinsa a matsayin dan kasa, Punch ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Anthony Ejiofor da kuma Jami’in Hulda da Jama’a, Basil Onwukwe ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Jawabin World Igbo Congress game da kame Mazi Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi’.

KARANTA WANNAN: Najeriya Ta Hada Kai da Majalisar Dinkin Duniya Don Samarwa Kasa Abinci Mai Kyau

Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Kungiyar ta kuma bayyana kamun na Kanu a matsayin "kamu ba bisa ka'ida ba da hadin bakin kungiyoyin kasa da kasa."

Wani yankin sanarwar ya ce:

“An kuma tabbatar mana da cewa an kame Nnamdi Kanu, dan kasar Ingila, a wata kasar da ba Ingila ba wacce ya yi tafiya zuwa cikinta da fasfo din Burtaniya.
“Sakamakon haka, wannan ya tayar da hankali saboda kame shi ba bisa doka ba da kuma ayyukan kungiyoyin asiri na kasa da kasa wanda ya keta ka'idar tsarin mika mutum.

Yadda aka kame Nnamdi Kanu

Wani rahoto na jaridar Daily Sun ya nuna cewa an kama Mazi Nnamdi Kanu a Jamhuriyar Czech.

A cewar rahoton, shugaban IPOB ya yi tafiya daga kasar Ingila zuwa Singapore saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba kafin ya tafi Jamhuriyar Czech a ranar Juma’ar da ta gabata, 25 ga Yuni.

Rahoton ya ambato wata majiya, inda ya ce akwai wani bayani da jami'an Jamhuriyar Czech suka ba gwamnatin Najeriya, wanda ya kai ga kame Kanu a birnin Prague.

KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Tabbatar da Nadin Manjo Faruk Yahaya

Wata Kungiyar Igbo Ta Bayyana Farin Ciki da Kame Nnamdi Kanu, Ta Bayyana Dalili

A wani labarin, Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, kungiyar zamantakewar Ibo, ta ce kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, zai kawar da yunkurin yakin basasa kuma ya kawo zaman lafiya a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

A yau ne Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, an kame shugaban na IPOB bayan guduwan da ya yi zuwa wata kasar waje.

Da take magana a kan sake kame Nnamdi Kanu, Ohanaeze Ndigbo ta ce ci gaban zai kawo karshen tashin hankali a kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.