'Yan kabilar Igbo sun Musulunta, sun kuma bayyana za su gabatar da bikin aurensu ta hanyar addinin Islama

'Yan kabilar Igbo sun Musulunta, sun kuma bayyana za su gabatar da bikin aurensu ta hanyar addinin Islama

- Aishat Ugochi Obi da angonta Nurudeen (Nicholas) Ikeocha za su yi aure kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a jihar Imo

- Idan zamu tuna, masoyan junan da za su yi auren sunnah din sun musulunta ne a jajircewar da suka yi kwanan nan

- Za a yi wannan gagarumin bikin ne a ranar 10 ga watan Afirilun 2020 a jihar Imo

Soyayya na da dadi amma idan aka hadu da wanda ake so nagari. Aishat Ugochi Obi da Nurudeen (Nicholas) Iekocha wadanda suka koma Musulunci a jihar Imo zasu yi aure. Za a yi gagarumin auren ne a ranar 10 ga watan Afirilun 2020.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wannan ne karo na farko da za a yi bikin Musulmai ‘yan kabilar Ibo a jihar baki daya.

'Yan kabilar Igbo sun Musulunta, sun kuma bayyana za su gabatar da bikin aurensu ta hanyar addinin Islama
'Yan kabilar Igbo sun Musulunta, sun kuma bayyana za su gabatar da bikin aurensu ta hanyar addinin Islama
Asali: Facebook

Kamar yadda wani ma’aboci amfani da Nairaland ya bayyana, duk da wasu na tsammanin duk ‘yan kabilar Ibo Kiristoci ne, toh hakan ba gaskiya bane.

“Ana ta yadawa cewa duk ‘yan kabilar Ibo duk Kiristoci ne, toh gashi yau ina sanar da ku auren farko na Musulmai. ‘Yan kabilar Ibo na da karamci. Mutane da yawa basu fahimci yadda ‘yan kabilar suke ba ne.” yace.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Mabiya addinin Hindu sun watsawa wani Limamin Masallaci guba a fuska

Za a yi bikin masoyan ne a Idem Ogwa. “Muna da ire-irensu Sheikh Abdullahi Adam Idoko, wanda shi ne babban limamin masallacin jami’ar Najeriya da ke Nsukka. Ustaz Isah Okonkwo, wanda ya yi limamin babban masallacin jami’ar Ibadan, Allhaji Abdulaziz Chibuzo Ude, wanda ya kirkiro kamfanin wallafa na Nok da sauransu.” Ya kara dacewa.

Amma kuma Legit.ng ta ruwaito cewa sananniyar ‘yar fim din Nollywood mai suna Ngozi Ezeonu an zargeta da aurar da diyarta mai suna Odechukwu Ediwa Ezeonu ba tare da sanin mahaifinta ba.

Diyar tayi aure na a ranar Asabar, 15 ga watan Fabrairu na 2020 a wani kayatacce kuma gagarumin biki da aka yi a garin Asaba na jihar Delta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng