Tun da Najeriya ta zama kasa guda a 1914 ba mu taba amfana ba - Inji SEMON
Mun samu labari cewa wata Kungiya ta Musulman Inyamuran Najeriya ta koka da halin da mutanen ta su ke ciki inda tace ba ta taba karuwa da Gwamnati tun da aka gama Najeriya a shekarar 1914 ba.
Kungiyar nan ta SEMON ta Musulman da ke Kudu maso Gabashin Najeriya tace ba su taba cin romon wata Gwamnati ba tun da ake a tarihi. Kungiyar tayi wannan jawabi ne a Ranar Asabar na karshen makon da ya wuce.
SEMON tace ana haramtawa Musulman kasar Inyamurai takara a Kudancin Najeriya, sannan kuma Gwamnatin Jiha ko ta Tarayya ba ta yi da su a sama. A dalilin wannan ne Kungiyar ta nemi ‘Ya ‘yan ta su fara neman takara.
KU KARANTA: PDP ta bayyana abin da INEC da APC ke kullawa a game da zaben 2019
Kungiyar tace kowa ya san Musulman da ke Kasar Ibo da bin doka da rashin tada hatsaniya kuma sun yi wa Gwamnatin Tarayyar Kasar mubaya’a. Sai dai duk da wannan, idan aka tashi raba mukaman siyasa sai a ware su gefe guda.
Shugaban Kungiyar ya kuma yabawa Gwamnatin Muhammadu Buhari tana kuma mai kira gare sa da ya cigaba da maganin miyagun barayi tare da kuma nada wadanda su ka cancanta a mukaman Gwamnati kuma ya guji kabilanci.
Dazu mun ji cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yace Gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo rabuwar kai da sabani a Najeriya da kuma kashe-kashe na gilla daga 2015 zuwa yau.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng