Wahalar man fetur a Najeriya
Duk da gwamnati ta janye tsarin tallafin man fetur, layin motoci da babura sun dawo. Akwai alamun cewa farashi zai iya canzawa, shiyasa gidajen mai su ka rufe.
Gwamnatin jihar Ekiti karkashin shugabancin gwamna Biodun Oyebanji ta fara raba N5,000 ga masu ƙaramin ƙarfi 7,000 da nufin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Yayin da farashin litar bakin mai ke kara ta shi, ana hasashen kamfanonin Dangote da BUA ka iya kara farashin kayansu saboda amfani da bakin mai din.
Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa farashin man fetur zai fadi daga N617 kan kowace lita a yanzu zuwa N180. Malamin ya bayyana hakan ne a cikin sabon sako.
Kamfanin mai na NNPC na bin gwamnatin Shugaba Tinubu bashin Naira tiriliyan bakwai na tallafin mai wanda gwamnatin ba ta iya biyan kamfanin ba na tsawon lokaci.
Na Allah ba sa karewa yayin da wasu masu gidajen mai su ka rage farashin mai zuwa Naira 430 ga masu babura da adaidaita sahu a jihar Borno don ragewa jama'a radadi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an dawo da tallafi yayin da Shugaba Tinubu ya biya Naira biliyan 169.4 don tsayar da farashin lita kan Naira 620 kacal.
Bayan dogon jiran lokacin da za ta fara aiki, matatar man fetur ta Dangote ta sanar da cewa a cikin watan Oktoba za ta fara aikin tace ɗanyen man fetur.
Kamfanin man fetur na ƙasa NNPCL ya girgiza ɓangaren ma'aikatansa, ya sanar da sallamar duk wanda ya rage masa kasa da watanni 15 ya yi ritaya daga aiki.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari