Wahalar man fetur a Najeriya
Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja da kuma wasu jihohin kasar nan sun nuna cewa farashin litar fetur ya kusa kaiwa N1000 yayin da wahalar mai ta tsananta.
Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya ce ya bankado tare da kwace mai daga wasu haramtattun matatun mai guda 63 da bututun satar mai 19 a yankin Neja Delta.
Farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron zabi a cikin birnin Kano. A yanzu an koma siyar lita kan kusa da N1000. Hakan na zuwa ne bayan gama zanga-zanga.
Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta nemi gwamnatin tarayya ta samar da kotu na musamman saboda barayin fetur don saukaka hukunci.
Matatar man fetur ta Fatakwal da ke Ribas ta gaza fara aiki a watan nan duk da alkawarin da shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya dauka na cewa za a fara aiki.
Rukunin kamfanonin Dangote ya fitar da sanarwa kan rahoton cewa matatar man Dangote ta kayyade farashin litar fetur. Kamfanin ya ce ikirarin IPMAN ba gaskiya ba ne.
Kasar Libya ta sha gaban Najeriya a cikin jerin kasashen nahiyar Afirika mafi yawan arzikin man fetur. Najeriya ta zo a matsayi na biyu a cikin jerin.
Tsohon mataimakin shugaban PDP, Bode George ya bukaci Bola Tinubu ya fadi gaskiya ga yan Najeriya kan maganar cewa ya dawo da tallafin man fetur a boye.
Mele Kyari, shugaban NNPC, ya ce kamfanin bai karya wata doka a mu’amalarsa da abokan hulda ba, don haka a daina alakanta su da zagon kasa na tattalin arziki.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari