Kwastam Ta Fadi Abin da Ke Kawo Karancin Man Fetur, Ta Kama Sama da Lita 150,000

Kwastam Ta Fadi Abin da Ke Kawo Karancin Man Fetur, Ta Kama Sama da Lita 150,000

  • Hukumar kwastam ta Najeriya ta yi bayani bayan mako biyu da ta shafe tana samame kan masu safarar man fetur zuwa ketare
  • Hukumar ta yi samamen ne kan iyakokin Najeriya ta sassa daban-daban domin gano barnar da ake tafkawa kan safarar mai
  • Har ila yau, hukumar ta bayyana adadin man fetur da ta kama tare da fadin yadda lamarin ke jawo karancin mai a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukumar kwastam ta kasa ta yi bayani kan nasarorin da ta samu cikin mako biyu bayan fara samame kan masu safarar man fetur.

Samamen na cikin kokarin hukumar na tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya da tabbatar da wanzuwar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa na neman mayar da ofishin mataimakin shugaban ƙasar Najeriya ya zama 2

Kwastam
Kwastam ta kama masu safarar man fetur a Najeriya. Hoto: Nigeria Customs Service.
Asali: Facebook

Hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa safarar man fetur zuwa ketare na jawo dimbin asara ga tarayyar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake safarar man fetur?

Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi ya ce masu safarar mai suna amfani da bambancin farashi da ke tsakanin Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita.

Bashir Adewale Adeniyi ya ce suna safarar man Najeriya suna kai shi kasashen ketare ne domin sayar da shi a farashi mai tsada.

Kwastam ta kama man fetur

Hukumar kwastam ta bayyana cewa cikin mako biyu da ta fara samame ta kama man fetur sama da lita 150,950 da kudinsa ya kai N105.9m.

A cewar hukumar, ta kama man fetur din ne a iyakokin Najeriya da ke jihohin Adamawa, Sokoto da Cross Rivers.

Illar safarar man fetur ga Najeriya

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi albishir yayin da ta bayyana ƙoƙarinta wajen shawo matsalolin Najeriya

Shugaban hukumar ya bayyana cewa safarar man fetur yana zama barazana ga tattalin arzikin Najeriya.

Ya kara da cewa yana daga cikin abubuwan da suke kawo karancin man fetur a Najeriya kuma zai iya haddasa matsalolin tsaro a iyakokin kasar.

An kama 'yan bindiga a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda reshen birnin tarayya Abuja sun kai farmaki maboyar yan bindiga a tsakanin Abuja da Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa bayan musayar wuta da aka yi, yan sanda sun fatattaki yan bindigar tare da kama shugabanninsu da kubutar da wadanda aka sace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel