Gwamnatin Najeriya
Tun fara mulkin farar hula a shekarar 1999 aka fara samun badakala a Najeriya. Cikin manyan abubuwa da suka faru akwai badakalar Salisu Buhari, tazarcen Obasanjo.
Majalisar Dattawa ta amince da dokar dawo da tsohon taken Najeriya "Nigeria We Hail Thee" tare da maye gurbin "Arise O Compatriots" domin kara kishin kasa.
Majalisar dokokin jihar Benue ta rusa dokar da aka kafa a 2023 da ta ba jihar umarnin biyan fansho da daukar dawainiyar tsofaffin gwamnoni har su mutu.
Yayin da duniya ke bikin ranar yara ta duniya, akasarin yara a Najeriya ba za su iya bikin wannan rana ba duba da kangin rayuwa da suke ciki a yanzu.
Kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Tinubu ta bukaci yan Najeriya su kara juriya domin ciyar da Najeriya gaba. Shugaban kungiyar, Dahiru Hammadikko ne ya yi bayanin
Kungiyar SERAP ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi amfani da bikin cika shekara daya a kan karagar mulki wajen bayyana yawan kadarorin da ya mallaka.
Gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban Kotun Koli a kan gwamnonin jihohin kasar nan 36 a kan zargin rashin da’a yayin gudanar da kananan hukumomi.
Osita Chidoka ya soki gwamnatin Najeriya a kan maido alaka da kamfanin Emirates. Ministan jirage ya hada jigon PDP da Atiku ya yi masu kifa daya kwala a dandalin X.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ta tsinci kanta a ciki a baya. Ya yi alkawari yi aiki tukuru.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari