Abu Ya Yi Kyau: An Kara Wa Yan Najeriya Damar Sayen Hannun Jari a Matatar Dangote

Abu Ya Yi Kyau: An Kara Wa Yan Najeriya Damar Sayen Hannun Jari a Matatar Dangote

  • Matatar Dangote ta ƙara wa’adin sayar da hannun jarinta da makonni biyu domin bai wa masu zuba jari daga ƙarin ƙasashen Afirka damar shiga
  • Aliko Dangote ya shirya sayar da hannun jarin guda biliyan 4.1 kan N525 kowanne, kuma ana sa ran za a tara sama da Naira tiriliyan 2
  • Ana shirin amfani da kuɗin da za a tara wajen ninka ƙarfin matatar zuwa ganga miliyan 1.4 a rana da faɗaɗa ayyukanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Matatar Man Feturin Dangote (DPRP) ta tsawaita wa’adin sayar da hannun jarint na farko ga jama’a (IPO) da makonni biyu.

Matatar ta dauki wannan matakin ne domin bai wa masu zuba jari daga wasu ƙasashen Afirka damar shiga tsarin da ake sa ran zai zama mafi girma a tarihin nahiyar.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tsohon Shugaban FRSC ta Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Matatar Dangote.
Daya daga cikin wuraren ajiyar mai a matatar Dangote da ke jihar Legas Hoto: Dangote Group
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa an buɗe sayar da hannun jarin a ranar 14 ga Satumba, kuma an tsara rufe shi a ranar 13 ga Oktoba. Sai dai matatar ta sanar da tsawaita wa’adin da wasu makonni biyu.

Dalilin sayar da hannun jarin matatar Dangote

Hannun jarin da ake sayarwa sun kai biliyan 4.1, inda kowanne zai kasance kan farashin Naira 525. A cewar kamfanin Dangote, ana sa ran cinikin zai tara sama da Naira tiriliyan 2.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana a baya cewa sayar da hannun jarin zai bai wa direbobi, masu girki, ’yan kasuwa, ma’aikata da manajoji damar mallakar kaso a matatar.

Dangote ya ce:

"Ba don samar da kuɗin faɗaɗa matatar kawai ake yin wannan ba, domin kuɗin ya fi haka yawa. Abin da muke ƙoƙarin yi shi ne tabbatar da cewa mafi yawan direbobinmu, masu girkinmu, ma’aikatanmu, manajojinmu da sauran mutane sun samu damar mallakar kaso a wannan matatar.”

Kara karanta wannan

Matatar mai: Ɗan takarar shugaban ƙasa a Kenya ya gargadi Dangote

Ya ƙara da cewa manufarsa ba ta tsaya ga tara kuɗin faɗaɗa matatar ba, domin ana son bai wa jama’a a faɗin nahiyar Afirka damar mallakar hannun jari a matatar mai mafi girma.

Mutane na kara nun sha'awar saye

A cikin wata sanarwa, matatar man ta bayyana cewa tana buƙatar ƙarin lokaci domin faɗaɗa damar shiga shirin ga masu zuba jari a ƙasashen Afirka daban-daban, cewar rahoton Leadership.

Dangote.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote lokacin kaddamar da shirin sayar da hannun jarin matatarsa Hoto: Dangote Group
Source: Facebook

Sanarwar ta ce:

“Tsawaita wa’adin zai taimaka wajen ci gaba da ƙoƙarin faɗaɗa damar shiga kasuwannin Afirka, ciki har da faɗaɗa hanyoyin rarraba hannun jarin da aiwatar da shirye-shiryen takardun shaidar hannun jari da za su sauƙaƙa wa masu zuba jari daga ƙasashe daban-daban shiga shirin.”

Ta ƙara da cewa tana farin ciki da yadda masu zuba jari suka nuna sha’awa zuwa yanzu, kuma tana ganin ƙarin lokacin zai bai wa mutane da dama a faɗin Afirka damar sayen jannun jarin.

Dangote ya ba daliban Najeriya dama

Kun ji cewa gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da shirin da zai bai wa daliban Najeriya karin hannayen jari 10 kyauta bayan sun sayi akalla guda 10.

Haka zalika, wannan shiri yana da nufin bunkasa ilimin harkokin kudi, zuba jari da kuma samar da arziki na dogon lokaci tsakanin matasan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262