Aikin Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ba a fahimce ta ba ne a kan kalamanta na kwanan nan da ke cewa za a kara kudin hasken wuta ga 'yan Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Abba Abubakar Aliyu a matsayin shugaban hukumar wutar lantarki ta karkara (REA.) Abba yana rike da REA tun daga Maris din 2024.
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya fito da sabon tsarin da zai ba shi damar tattaunawa da mazauna jihar a dukkanin kananan hukumomi kai tsaye.
Hukumar daukar ma'aikata ta kasa ta sanar da matasan kasar nan da su karkade takardunsu domin neman guraben aikin da ta ware domin rahe rashin aiki.
Kungiyar CNPD ta gano kuskure a sabon tsarin rabon harajin VAT da gwamnonin Najeriya suka gabatar, yayin da ta yaba wa Shugaba Tinubu kan kudurin gyaran haraj.
Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ana ci gaba da daukar matakan da za su tabbatar da ingancin ilimi a jihar, daga cikinsu shi ne kara kudin ciyar da daliban makarantu.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin ɗaukar Hassana Nazifi, makauniyar da ta kammala digiri a BUK aiki nan take, ya ce za a naɗa ta muƙami.
Kungiyar kwadago ta NLC ta bukaci ministan lantarki Bayo Adelabu ya yi murabus saboda gaza magance matsalolin wuta a Najeriya. NLC ta ce bai kware ba sam.
Gwamnati za ta dauki matasa masu shekara 25 zuwa 35 domin su yi aiki a ƙananan hukumomi 774 karkashin shirin kiwon lafiya na NHFP. An kafa sharudda.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari