Zaben Najeriya
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kama wata dattijuwa yar shekara 73 da wasu mutum biyu bayan samunsu da katin PVC 20 a Benin
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya ce jam'iyyarsu ta PDP za ta karbi sakamakon zaben da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu da tsarkakkiyar zuciya.
Wata baiwar Allah mai ɗauke da juna biyu, Shamsiyya Ibrahim, ta yanke jiki ta fadi a layin zabe a Tsafe, Allah ya mata cikawa yayin da aka kaita Asibitin garin.
Hukumar EFCC ta kama wani malamin jami'a mai suna Dakta Cletus Tyokyya da tsabar kudi har naira miliyan 306 a rumfar zabe da ake zargin na siyan kuri'a ne.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya samu nasararsa ta farko a zaben shugaban kasa Najeriya dake gudana yau Asabar a fadin tarayya. Kwankwaso ya lashe rumfarsa..
Gwamnan na Kaduna Ya Bayyana cewar Yadda Jama'a Sukayi Kamfo a Runfunan Zabe Abu ne Mai Ci Masa Tuwo a Kwarya Duk da Yabawa INEC Abisa Amfani da Naurar BVAS
Yayin da yan Najeriya suka fito don yin zaben shugaban kasa a yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu, wasu yan daba sun farmaki rumfar zabe a yankin Ikate dake Lagas.
Wasu yan daba da ake zargin na PDP sun yi kokarin tilasta mutane zaben jam'iyyarsu sun tarwatsa rumfar zabe tare fasa akwati duk da kasancewar yan sanda a wajen
Jam'iyyar Accord ta janye daga zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu inda ta ayyana goyon bayanta ga Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.
Zaben Najeriya
Samu kari