Yan Daba Sun Fasa Akwatunan Zabe, Yan Sanda Sun Tarwatsa Kowa Da 'Tear Gas'

Yan Daba Sun Fasa Akwatunan Zabe, Yan Sanda Sun Tarwatsa Kowa Da 'Tear Gas'

  • Jihar Akwa Ibom ta shiga jerin jihohin da aka tayar da hatsaniya a zaben shugaban kasan dake gudana
  • Wasu yan baranda da ake zargin na PDP ne sun tayar da tarzoma saboda wasu sun ki zaben jam'iyyarsu
  • Jami'an yan sanda sun tarwatsa kowa daga wajen kuma an fasa akwatin zabe da kuri'un da aka kada

Akwa Ibom - An dakatar da zabe a Unit 1, Ward 10, makarantar firamaren Ebom, karamar hukumar Itu a jihar Akwa Ibom biyo bayan rikicin da ya barke a wajen.

Vanguard ta ruwaito cewa wakilan jam'iyyar PDP ne suka haddasa rikicin inda suke kokarin hana wasu zaben dan takarar da ba na PDP ba.

Ma'aikatan wucin-gadin INEC tuni suka arce daga wajen.

Jami'ar yar sandan dake wajen ita ma ta arce daga wajen yayinda ta ga abin ya fi karfinta.

Kara karanta wannan

Yan Daba Sun Kai Farmaki Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe A Bauchi

Akwa Ibom
Yan Daba Sun Fasa Akwatunan Zabe Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mai zabe wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya yi bayanin cewa suna kan layi ne kuma suka lura ana kokarin tilasta mutane zaben yan takarar PDP kadai.

Yayinda masu zaben suka ce basu yarda ba, yan PDP suka tada hatsaniya a wajen.

Jami'ar yar sandan da ta gudu da farko ta dawo da dimbin abokan aikinta wadanda suka watsawa kowa a wajen barkonon iska kuma suka tarwatsa kowa.

Tuni dai an fasa akwatunan zabe.

Yan Tada Zaune Tsaye a Gombe Sun Farmaki Ma’aikatan Wucin-Gadin INEC a Gombe

Yau take ranar da yan Najeriya suka dade suna jira na tsawon shekaru hudu domin gudanar da zaben kasa da aka saba duk bayan shekara hudu.

Zaben na bana yazo da sabon salo, kalubale da kuma tashin-tashina wacce ba’a zata ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abin Da Yasa INEC Bata Tura Sakamakon Zabe Yanar Gizo Kai Tsaye Ba, Jigon APC

Gwamnati ta takaita yawan kudade dake yawo a hannun jama’a domin hana siyan kuri’u da yan siyasa ke yi, sai kuma zancen hare-hare da ake kaiwa ofisoshin yan sanda dake kudu maso kudu da sauran sassa daban daban na kasar dake fama da matsalar rashin tsaro.

Ana tsaka da haka ne kuma duk dai a yau din, mahara da ba’a san ko su waye ba suka farmaki wasu ma’aikatan wucin-gadin INEC yayin da suke tunkarar wajen aikin da aka tura su a jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel