Daura
A yau Asabar 9 ga watan Nuwamba ne dan uwan Shugban kasa Muhammadu Buhari, Mamman Daura ya cika shekaru 80 da haihuwa kuma daya daga cikin 'ya'yan sa, Fatima ta yi amfani da wannan dama ta yi wallafa wani rubuta inda da ta sadauka
Sarkin Daura ya fito ya yi na’am da biyayyar da Yemi Osinbajo ya ke yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yace an jarraba mubaya’ar da Osinbajo yake yi wa Buhari kuma an gamsu.
Mun ji cewa Manyan kasa sun halarci nadin sarautar ‘Danuwan Buhari a Daura inda shi kuma shugaban kasar yake Landan ya na hutawa a Turai.
A halin yanzu sabon rikici ya barke da Matar Shugaban kasa da ‘Ya ‘Yan Mamman Daura kumar har wasu sun fara kira ga Majalisa da binciki rikicin da ake yi a cikin Fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Darajar Shugaban kasa ta sa ana yin wasu aikace-aikace a Daura. Daga cikin hanyoyin da aka gama akwai titin da ya tashi tun daga Fago-Katsayal-Kwarasawa Jirdere-Koza to Kawanar Sabke da Sandamu-Baure.
A ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 1987 ne gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kirkiro jahar Katsina daga cikin jahar Kaduna, wanda hakan yasa a yanzu Katsina ta cika shekaru 32
Dazu nan mu ka ji cewa wani Tsohon Ma’aikacin Shugaba Buhari, Nalado Sandamu, ya rasu. Sandamu wanda ya shafe shekaru ya na yi wa Buhari hidima ya mutu a asibitin AKTH a Kano jiya Litinin.
Yankin karamar hukumar Daura da ke jihar Katsina tace ta kashe naira miliyan 1.4 domin gyara burtsatse a unguwanni 11 da ke yankin domin bunkasa hanyan samar da ruwa.
Ruwan dare ya rusa gidaje fiye da 100 a Daura da ke Jihar Katsina. Gidajen mutane sama da 100 sun ruguje a dalilin wannan ruwa mai karfi da aka fara tun safiyar Ranar Lahadi inda ya yi ta kwarara har dare.
Daura
Samu kari