Tsantseni: Yadda karamar hukumar Daura ta gyara 'burtsatse' 26 da N4.1m

Tsantseni: Yadda karamar hukumar Daura ta gyara 'burtsatse' 26 da N4.1m

Yankin karamar hukumar Daura da ke jihar Katsina, tace ta kashe naira miliyan 1.4 domin gyara burtsatse a unguwanni 11 da ke yankin domin bunkasa hanyan samar da ruwa.

Alhaji Hamisu Nuhu, Kansila da ke kula da harkar ruwa, gyara da tsafta a yankin ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Daura a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba.

Nuhu ya bayyana cewa hukumar ta sauya kayayyakin birtsase da suka lalace domin tabbatar da samun ruwa ba tare da an sha wahala ba a unguwannin da abun ya shafa.

Yace an kammala rukunin farko na aikin a farashi mai sauki cikin kasa da wata guda.

KU KARANTA KUMA: Neman a zauna lafiya ya sa Jonathan bai hukunta Buhari ba kan haifar da rikici a babban zaben kasa na 2011 - Adoke

Nuhu ya bayar da tabbacin cewa sauran garuruwa ma za su amfana daga aikin a rukuni na biyu, wanda ake shirin faraway kwanan nan, inda ya kara da cewa an riga an kammala tattara sunayen wadannan garuruwa.

Yayi kira ga garuruwan da suka amfana da su lura da sanya idanu akan yadda ake tafiyar da ruwan ta kwamitin yankunansu da aka rigada aka kafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel