Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

A yau Asabar 9 ga watan Nuwamba ne dan uwan Shugban kasa Muhammadu Buhari, Mamman Daura ya cika shekaru 80 da haihuwa kuma daya daga cikin 'ya'yan sa, Fatima ta yi amfani da wannan dama ta yi wallafa wani rubuta inda da ta sadaukar masa. Ta bayyana wasu muhimman abubuwa da mutane da dama ba su sani a kan mahaifinta.

Ga dai wasu batuttuwa 5 da ta fadi a kan mahaifinta kamar yadda The Cable ta ruwaito.

1. Yana da da na miji daya ne tak kamar Buhari

Daura da Buhari sunyi kamanceceniya a fanoni daban-daban kuma ranar Asabar din Fatima da bayyana cewa aminan biyu duk suna da 'ya'ya maza daya ne taka yayin da kuma suna da 'ya'ya mata masu yawa.

A cikin rubutun ta kuma ce a mahaifinsu baya fifita dansa na miji kan matar kamar yadda wasu ke yi.

2. Mata daya tak ya ke da shi

Akasin yadda yadda mafi yawancin maza a arewa ke auren mata fiye da daya, Mamman Daura mace daya tak ya aura, Ummu Kulthum kuma suna da 'ya'ya mata biyar da 'da na miji daya da jikoki 14.

A cikin rubutun da Fatima ta sadaukarwa mahaifinta, ta ce ba ta taba ganin ya yi fada da matarsa ba kuma bacin rai bai taba sa shi yunkurin kara aure ba.

Ta ce, "Baba baya fushi - Bana tsamanin cikin shekaru 40 da 'yan kai na taba jinsa yana daga murya ko yi wa wani fadi ba ko da akwai bukatar hakan. Baba ba ya daga muryarsa ga mutane har da masu masa hidima a gida.

3. Yana nuna wa 'ya'yansa da matsarsa kauna

Daura ya na nuwa wa matarsa da 'ya'yansa kauna. Ya kan yi wasa da su har wasu lokutan ya kan zuba musu abinci kafin ya ci nasa a abincin a cewar Fatima.

Ta ce mahaifinsu ya kan yi wasanni da su kamar na 'riyo-riyo' har sai ya gaji ya kyalle su.

4. Ya shiga mawuyacin hali a zamanin mulkin Obasanjo

Sauye-sauyen da sabon gwamnatin Obasanjo ta yi a 2000s sun jefa shi cikin mawuyacin hali a cewar rubutun da ta wallafa. Sauye-sauyen sun janyo rushewar kamfanoni wadda hakan ya jefa Daura cikin mawuyacin hali.

Sai dai ta ce duk da halin da ya shiga bai taba cire tsammani ba kuma ya kan koyar da 'ya'yansa muhimmanci hakuri da juriya.

5. Wuraren da ya yi karatu

Tsohon mai tace labaran a jaridar New Nigerian ya fara karatunsa ne a Katsina Middle School sannan ya yi sakandare a Kwalejin gwamnati da ke Okene a jihar Kogi. A karshen 1950s yana daya daga cikin tsirarun matasa masu hazaka a arewa da Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello ya tura karatu Ingila.

Daura ya karanci Harshen turanci, adabin turancin, harshen Latin da kundin tsarin mulkin Britaniya a Kwallejin Bournemouth. Ya kuma samu ikon shiga Kwallejin Trinity mai daraja a Dublin inda ya yi digirin farko a nazarin tattalin arziki da siyasa da kuma digiri na biyu a nazarin mulkar al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel