Bidiyon Aisha Buhari a cikin Aso Villa ya na cigaba da jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Bidiyon Aisha Buhari a cikin Aso Villa ya na cigaba da jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Akwai alamun sabuwar rigima ta barke tsakanin Mai girma matar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma ‘Yanuwan Malam Mamman Daura wanda ‘Danuwa ne wurin shugaban kasa.

A farkon makon nan ne wata ‘Diyar Mamman Daura mai suna Fatima, ta yi hira da gidan jaridar BBC Hausa inda ta kwashe duk labarin sabanin da ke tsakaninsu da Uwargidar shugaba Buhari.

Fatima Mamman-Daura ta bayyana cewa ita ce ta dauki hoton wannan bidiyo da ya rika yawo a gari inda aka ji muryar Hajiya Aisha Buhari ta na ta faman banbami a cikin fadar shugaban kasar.

A cewar Fatima Daura, ta dauki wannan bidiyo ne ya zama hujja a gare ta lokacin da su ka samu takkadama da matar shugaban kasar kwanakin baya a dalilin tada su da aka yi daga wani daki.

A na ta bangaren Aisha Buhari ta bayyana abin da ya faru inda tace babu shakka ita ce a wannan bidiyo tare da Masu gadinta wanda gwamnati ta bata amma su ka ki daukar mataki a kan Daura.

KU KARANTA: Jagororin Ibo za su sa-labule da Shugaban kasa Buhari a Aso Villa

Matar shugaban kasar ta zargi Jami’an tsaron Aso Villa da kin hukunta Fatima Mamman Daura a lokacin da ta ke daukar wannan bidiyo lokacin da ta ke yunkurin shiga sashensu da su ka rufe.

Hajiya Buhari take cewa ta yi yunkurin shiga dakin da aka ba Yusuf Buhari ya yi jinya ne sai ta iske ‘Ya ‘yan Mamman Daura duk sun rufe wannan kofa inda tace wannan ya sa ta wannan fushi.

Wasu su na ganin bai kamata tun farko Iyalan Mamman Daura su hakince a cikin Aso Villa ba. Kungiyar CDNDC ta nemi majalisa ta binciki lamarin inda tace ana amfani da fadar bai daidai ba.

Shi kuma shugaban kungiyar CACOL, Debo Adeniran, a wata hira da ya yi da jaridar Punch, ya na ganin ba haka ba inda yace babu komai don ‘Yan uwan shugaban kasa su na zama a cikin fadar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel