Yadda Mamman Daura ya ke bada umarni da sunan Shugaban kasa – Inji Aisha Buhari

Yadda Mamman Daura ya ke bada umarni da sunan Shugaban kasa – Inji Aisha Buhari

A yau, mu ka samun labari cewa Uwargidar shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta fito ta bayyana yadda Mamman Daura ya ke ba Hadiman shugaban kasa umarni.

A wani dogon jawabi da ya fito daga bakin Mai dakin shugaban kasar dazu, ta fallasa yadda ‘Danuwan shugaban kasa, Mamman Daura ya ba Garba Shehu umarnin fitar da jawabin soke ofishinta.

Aisha Buhari ta ce Shehu da ya fitar da jawabin cewa wannan gwamnati ba za ta yi aiki da ofishin Matar shugaban kasa ba, shi ne ya fadawa wani Hadimin ta cewa Mamman Daura ya sa shi wannan aiki.

Uwargidar shugaban kasar ta rubuta takarda ne mai taken Garba Shehu ya wuce inda ya kamata ya tsaya. Wannan takarda ta shiga hannun ‘Yan jarida ne a safiyar Ranar 11 ga Watan Disamban 2019.

Matar Shugaban ta zargi Mai magana da yawun bakin Mai girma Buhari da shiga sharo babu shanu, ta hanyar kutsawa cikin sha’anin Iyalin shugaban kasar. Wanda ta ce ya jawowa jama’a abin kunya.

KU KARANTA: Abin da ya sa Buhari ya ki karawa Shugaban FIRS wa'adi

Hajiya Buhari ta ce shisshigin da Hadimin Mai gidan na ta ya ke yi cin amana ce. “Ya manta cewa sha’anin Uwargidar shugaban kasa wata al’ada ce ta riga ta zama shiri mai zaman kanta a Najeriya.”

“Yau ko da babu kasafin sisi, ina gudanar da harkoki na na taimakawa al’umma. A inda aka cigaba, Garba Shehu zai ajiye aiki ne ba tare da wata-wata ba, bayan wannan wuce gona da iri.” Inji ta.

“Ganin rashin biyayyar gaskiya na Garba Shehu ga shugaban kasa ya jawo duk yardar da ke tsakaninsa da Iyalina ya ruguje saboda abin irin kunyar da ya jawowa fadar shugaban kasa da Iyalinsa”

“Abin da ya yi kwanan nan shi ne yakar Iyalin shugaban kasa ta hanyar kitsa mani sharri ta kafafen yada labarai na karya domin su yi wa ni da ‘Ya ‘ya na kazafi.” Shehu ya guji maida martani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

Source: Legit.ng

Online view pixel