Hukumar Immigration ta gina sabon cibiyarta a kan N145m a mahaifar Buhari

Hukumar Immigration ta gina sabon cibiyarta a kan N145m a mahaifar Buhari

Hukumar kula da shige da fice, watau Immigration, ta kaddamar da wani katafaren sabon sansaninta da ta gina a garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake jahar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwanturolan hukumar na kasa, Mohammed Babandede ne ya jagoranci kaddamar da sansanin, inda yace sun gina sansanin ne domin yaki da ayyukan yan bindiga, masu safarar mutane da kuma shigowar bakin haure cikin Najeriya.

KU KARANTA: Siyasa mugun wasa: An cigaba da tone tonen asiri tsakanin manyan gwamnanonin PDP 2

Babandede ya kara da cewa a baya jami’an hukumar dake aiki a kan iyakokin Najeriya basu da wata sansani ko cibiya da zasu dinga taruwa suna tsara yanayin aikinsu, wannan ma yana daga cikin dalilan da yasa hukumar ta gina wannan sabon sansani.

Babandede wanda ya samu wakilcin mataimakin kwanturola Idris Jere ya bayyana cewa: “Wannan sansani tare da sauran sansanoni dake kan iyakokin Najeriya an ginasu ne domin jami’anmu su yi amfani dasu wajen tsara ayyukansu.

“Haka zalika domin su dinga tattara bayanai suna aika ma shelkwatar hukumar dake babban birnin tarayya Abuja, domin ta haka ne za’a dinga samun bayanan da suka dace tare da yanke shawarar daya kamata domin karfafa tsaron kasa.” Inji shi.

Shi ma a nasa jawabin, gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jahar Katsina, Mustapha Inuwa ya bayyana cewa samar da wannan sansani zai inganta aikin hukumar Immigration wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A wani labarin kuma, akalla mutane 19 ne suka gamu da ajalinsu a sakamakon wani mummunan hadari daya auku a kan babbar hanyar Funtua zuwa Zaria, a jahar Katsina, inda mutane da dama suka samu munanan rauni.

Hatsarin ya auku ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba da misalin karfe 8 na dare a daidai marabar Maska inda motoci guda uku suka yi arangama, motocin sun hada da Tankar mai, Sharon da Bus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng