Daura: Mataimakin Shugaban kasa ya halarci nadin 'Dan Madami

Daura: Mataimakin Shugaban kasa ya halarci nadin 'Dan Madami

A jiya Ranar Asabar aka yi bikin nadin sarautar ‘Dan Madamin Garin Daura. Wannan biki ya sa jama’a sun ga mataimakin shugaban kasa, Shugaban Majalisa, Gwamnoni da sauran manya.

Kamar yadda mu ka samu rahoto a Ranar 2 ga Watan Nuwamba 2019, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar, ya nada Alhaji Musa Haro a matsayin ‘Dan Madamin Daura na kasar Daura,

Manyan jami’an gwamnati da su ka hada har da mai girma mataimaikin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun shiga Garin na Daura domin wannan babban bikin nadin sarauta da aka yi.

Yemi Osinbajo ya na tare da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari a wajen wannan kasaitaccen biki da aka shirya jiya.

KU KARANTA: Takarar Shugaban kasa a zaben 2023 ta fara raba kan ‘Ya ‘yan PDP

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai da mataimakin gwamnan Katsina, Mannir Yakubu sun halarci wannan nadi da Mai martaba Sarki Faruk ya yi wa Musa Haro na ‘Dan Madamin Daura.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da kuma shugaban hukumar tsaro na NIA, Ahmed Rufai su na cikin wadanda su ka halarci wannan biki.

Haro Musa mai shekaru 44 shi ne wanda aka ba wannan babbar sarauta ta ‘Dan Madami wanda ta na cikin manyan sarauta a Masarautar Daura. Haro ya na cikin dangin shugaban kasa Buhari.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto cewa Alhaji Haro, ‘Da ne wurin Alhaji Haro Lamido da Hajiya Rakiya Danbafale. Rakiya Danbafale ‘yaruwa ce wurin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel