Buhari ya yi murnar cikar ‘Danuwansa Malam Mamman Daura shekara 80
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya aika sakon farin cikinsa ga ‘Danuwansa Malam Mamman Daura wanda ya cika shekaru 80 da haihuwa a Ranar Asabar, 9 ga Watan Nuwamba.
Dattijon kasar Mamman Daura ya cika shekaru 80 a karshen makon nan ne. Daya daga cikin ‘Yaruwar shugaban kasar Najeriyar ta haifi Mamman Daura shekaru 80 da su ka wuce a Daura.
A wani jawabi da Buhari ya fitar ta bakin Mai magana da yawun bakinsa, Malam Garba Shehu, ya ce kokarin Daura ya shiga cikin littafin tarihin cigaban Najeriya da ba za a manta da shi ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ke cewa har gobe za a cigaba da tunawa da yabawa dawainiyar da Dattijon ‘Danuwa kuma tsohon Amininsa ya yi wajen tarbiyar iyali da taimakon Najeriya.
A Ranar farin ciki na bikin taya Baba Mamman Daura murnar cika shekara 80 a Ranar 9 ga Watan Nuwamban 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga sahun duka mutanen dangi da Abokan gawurtaccen ‘dan jarida wajen murnar wannan rana, ina taya sa murnar shekarun da ya yi na kauna da sadaukar da kai ga Najeriya, musamman a bangaren aikinsa na jarida.
KU KARANTA: An kai karar Buhari kotu a kan wasu makudan kudi tun na 1999
Cikin farin ciki, shugaba Buhari ya na tuna basirar Daura tun yana karami a Makarantar Middle ta Katsina da kuma kwalejin gwamnati, inda wannan ya sa gwamnatin Arewa ta dauki dawainiyar karatunsa a kasar Birtaniyya a shekarun 1950s zuwa gaba, tare da cewa an ga basirar ilmin da ya samu.
Shugaban kasar ya na taya gawaurtaccen ‘dan jaridar kuma makarancin wanda ya yi aiki a gwamnati kafin ya koma gidan jaridar New Nigerian inda ya zama Edita har zuwa babban Manaja kafin ya koma kasuwanci ya kuma bunkasa tattalin Arewa ta harkar shiga harkar kayan daki, tufafi da karafuna da sauran hanyoyi.
Shugaban kasar ya kara jawabin na sa da rokon Ubangiji ya karawa Dattijon karin shekaru domin ya cigaba da dagewa kana bin da ya sa a gaba watau taimakon jama’a, musamman kyauta.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng