Sarkin Daura ga Osinbajo: An gamsu da biyayyar da ka ke yi wa Buhari

Sarkin Daura ga Osinbajo: An gamsu da biyayyar da ka ke yi wa Buhari

Mai martaba Sarkin Daura, Umar Farouk Umar, ya yaba da irin biyayyar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ke yi wa Mai gidansa watau shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sarki Alhaji Umar Farouk Umar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ke bayani a game da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin shugaban na Najeriya, Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo.

An rahoto Sarkin ya na yin wannan magana ne a wajen bikin nadin sarautar ‘Dan Madamin kasar Daura wanda aka yi a karshen makon nan inda manyan kasa da dama su ka samu halarta.

Sarkin Dauran ya ke cewa an jarraba mubaya’ar da Osinbajo yake yi wa Buhari kuma a cewarsa, irin wannan gaskiya da jajircewa da kuma sadaukar da kai a ke bukata domin Najeriya ta cigaba.

KU KARANTA: Osinbajo, SGF, COS da Gwamnoni sun shiga Daura domin nadin sarauta

Mai martaban yake cewa: “Mu na sane da halin da shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo, su ka samu Najeriya, amma yau, abubuwa su na canzawa a sakamakon kokarin da su ke yi.”

“Wannan bai rasa alaka da kyakkayawar huldar da aka samu tsakanin shugaba Buhari da mataimakin shugaba Farfesa Osinbajo, wanda aka dade ba a samu irin wannan tarayya ba.”

“Alakarsa da Buhari ta kasance daram-dam ne saboda gaskiyarsa, na jinjina maka mataimakin shugaban kasa. Ni a kashin kaina ina murna da yadda Osinbajo ya nunawa Buhari biyayya.”

Sarkin na Daura ya kare jawabinsa da cewa: “Masarautar Daura ta na godiya da kokari na tsaya tsayin dakan da ka yi wajen ganin ka kawo sauyi a Najeriya duk da tasgarorin da ake samu.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel