Tsohon Ma’aikacin Buhari, Nalado Sandamu, ya rasu jiya a asibiti

Tsohon Ma’aikacin Buhari, Nalado Sandamu, ya rasu jiya a asibiti

Mun samu labari wani daga cikin amintattu kuma masu amanar Barorin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu. Wannan Bawan Allah ya bar Duniya bayan shekaru 30 tare da Buhari.

Kamar yadda mu ka samu labari dazu nan, Alhaji Nalado Sandamu wanda aka fi sani da ‘Commander’ a wajen shugaban kasa Buhari ya cika ne a farkon makon nan a asibiti AKTH na Kano.

Nalado Sandamu ya kasance Mai rikon amana da gaskiya inji shugaban kasar. Sandamu ya rasu ne a asibitin koyon aiki na Malam Aminu Kano da ke cikin Garin Kano a Ranar Litini, 9 ga Satumba.

Marigayin ya kasance yana aiki a gidan shugaba Buhari da ke Daura a jihar Katsina. Majiyar ta ce shugaban kasar ya koka da rashin mutum mai gaskiya irin Nalado Sandamu, tare da addu’a ya cika da kyau.

KU KARANTA: An dakatar da batun bizne tsohon Shugaban kasar Zimbabwe

“Na rasa mai kula, mutum mai tsantsani kuma mai dadin sha’ani wanda ya rika lura da gida na a. Allah ya jikansa kuma ya ba Iyalinsa hakurin jure wannan babban rashi. Amin.” Inji Buhari

Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ta’aziyya ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu. Bayan sakon ta’aziyya, shugaban kasar ya aika jama’a ga iyalin Marigayin a Katsina.

Wadanda aka tura daga fadar shugaban kasa domin ta’aziyya sun hada da babban Hadimin cikin gida, Sarki Abba, Garba Shehu da kuma babban jami’in fadar shugaban kasa, Amb. Lawal Kazaure.

Mai kula da gidan shugaban kasa, Saleh Yuguda yana cikin babban Tawagar ta’aziyyar. Ana makokin Marigayin ne a ainhin Garinsa na Sandamu da ke kusa da Daura a Arewacin Katsina.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel