Yaba kyauta tukwici: Dalibi ya raba ma tsofaffin Malamansa motocin alfarma a Daura

Yaba kyauta tukwici: Dalibi ya raba ma tsofaffin Malamansa motocin alfarma a Daura

Kimanin kwanaki 10 da suka gabata ne aka yi bikin murnar cikar kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Daura jahar Katsina (FGC Daura) shekaru 30 da kafuwa, taron daya samu halartar dururuwan tsofaffin dalibai da malamansu.

A yayin taron ne wani tsohon dalibin makarantar ya nuna bajinta, tare da fitar da tsofaffin daliban makarantar kunya, inda ya baje kolin wasu tsala tsalan motocin alfarma guda 7 domin rabarwa ga wasu tsofaffin malamansa.

KU KARANTA: Buhari ya gargadi yan siyasa: Kada wanda ya saka ni a cikin sabgar siyasar a 2023

Yaba kyauta tukwici: Dalibi ya raba ma tsofaffin Malamansa motocin alfarma a Daura
Yaba kyauta tukwici: Dalibi ya raba ma tsofaffin Malamansa motocin alfarma a Daura
Asali: Facebook

Wannan dalibi ba wani bane illa Dakta Aminu Abdullahi Shagali, Kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, kuma shugaban kungiyar kaakakin majalisun dokokin jahohin Arewa gaba daya.

Da yake mika motocin ga Malaman ta hannun wakilinsa a yayin taron, Shagali ya bayyana farin cikinsa da ganin wannan rana, sa’annan ya yaba da kokarin da Malaman suka yi a kansa lokacin da yake dalibin makarantar.

Legit.ng ta ruwaito wasu daga cikin Malaman da suka samu wadannan motoci sun hada da tsohon shugaban kwalejin Alhaji Rabe Musa, Mista Towolawi, Malam Tukur Matazu, Malam Bashir Batsari, Malam T.S Sulaiman, Malam Zayyad da Malam Yusuf Birchi, sai kuma wani tsohon abokinsa shima tsohon dalibin makarantar.

Malaman da suka samu wadannan kyaututtuka sun bayyana farin cikinsu, tare da fatan Allah Ya saka ma wannan dalibi nasu da albarka

Baya ga motocin, Shagali ya raba ma Malaman kudin shan mai, haka zalika ya aika da sakon kudade ga iyalan tsofaffin Malaman makarantar da suka rasu, sai kuma suma malaman dake makarantar a yanzu sun samu ihisanin.

Bugu da kari kaakakin ya dauki nauyin gudanar da manya manyan ayyukan more rayuwa a cikin makarantar domin amfanin dalibai, malamai da ma sauran al’ummar makarantar, kamar su gyaran dakin karatu, famfunan ruwa, da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel