Murnar cikar Katsina shekaru 32: Jama’an Daura sun nemi a basu takarar gwamna

Murnar cikar Katsina shekaru 32: Jama’an Daura sun nemi a basu takarar gwamna

A ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 1987 ne gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kirkiro jahar Katsina daga cikin jahar Kaduna, wanda hakan yasa a yanzu Katsina ta cika shekaru 32 da kirkira.

Sai dai a yayin da ake murnar cikar jahar Katsina shekaru 32, al’ummar yankin masarautar Daura sun koka game da wariya da ake nuna musu a harkar siyasar jahar, don haka suka nemi a basu takarar shugabancin gwamnatin jahar a zaben shekarar 2023.

KU KARANTA: Mugunta ruwan fakko: Uwargida ta kashe jaririn kishiyarta da fiya fiya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cikin wata sanarwa da Ahmed Ahidjo Wali da Sada Bawa suka fitar a cikin wata talla sun bayyana cewa tsawon shekaru 32 ana nuna ma yankin Daura wariya tare da mayar dasu saniyar ware a siyasar jahar duk kuwa da cewa sun bayar da gudunmuwa ga cigaban jahar tsawon shekarun.

Don haka suka nemi masu ruwa da tsaki a jahar Katsina cewa ya kamata a yanzu a duba yankin Daura kuma a basu goyon baya domin su samar da gwamnan jahar Katsina a shekarar 2023. Sai dai wannan kiraye kiraye bai yi ma jama’an yankin Karaduwa da cikin Katsina dadi ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin kungiyar Katsina state progressive Movement, Mohammad Danjuma ya fitar da wata sanarwa a madadin yankin Katsina, inda yake cewa bai kamata jama’a su fara irin wannan magana ba, musamman a yanzu da ake gudanar da mulki bayan kammala zabe.

“Suna da shugaban kasa, kuma yana kan kai musu abubuwan cigaba da dama kamar su jirgin kasa, jami’ar gwamnatin tarayya ta sufuri, kwalejin kimiyya na gwamnatin tarayya, asibitin Sojojin sama, cibiyar horas da jami’an kwana kwana da sauransu, toh me suke nema kuma?” in ji shi.

Shi ma wani jagoran yan siyasa daga shiyyar Funtuwa, watau Karaduwa, Bala Abubakar ya mayar da martani inda yake cewa:

“Ba laifi bane su nemi a basu wannan dama, amma su sani a duk kasar nan babu masu morewa kamar yankin Daura, idan ana maganan kuri’u ne, yankin Funtuwa ta fi Daura bayar da kuri’u, duk Najeriya mune na biyu, don haka mun fi so a duba cancanta ba wai karba in karba ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel