Dandalin Kannywood
Batun rigimar sarkin waka da Nafisa Abdullahi, duk da dai wadanda suka fara rigimar sun yi shiru, wasu cikin 'yan masana'antar shirya fim basu bar magana ba.
Mawakin shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan yan siyasar arewa, Dauda Kahutu Rarara, ya caccaki gwamnati mai ci kan matsalar tsaro a wata sabuwar waka.
Babanchinedu ya caccaki Naziru sarkin waka kan kalaman da ya yi game da Nafisa saboda ta kalubalanci iyaye masu haihuwar yara suna sakinsu da sunan almajiranci.
Jaruma Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ‘ya’yansu almajiranci.
Maryam Booth ta kalubalanci Naziru da mayarwa malaman da suka yi wa'azi kan haihuwar yara ba tare da halin kula da su ba martani kamar yadda ya yi ma Nafisa.
Naziru ya ce cikin masu zagin almajiranci wasu ko cikakkiyar Fatiha ba za su iya kawowa ba amma suke zagin wadanda a cikinsu harda wanda ya rubuta Al-Kur'ani.
Jaruma Nafisa Abdullahi bata yi kasa a guiwa ba ta yi wa mawakin martani inda ta kira shi da mai neman suna. Idan kuma ya isa, ya ya bugi kirji ya kira suna ne.
A kan batun jaruma Nafisat Abdullahi kuwa, jama'a sun yi caa a kanta bayan ta caccaki iyaye masu haifar 'ya'yan da basu kula da su ko suke tura su almajiranci.
Fitaccen mawakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara, ya bai wa Furodusa Abba Abubakar Mai Shadda kyautar dalleliyar mota sabuwa kirar Honda.
Dandalin Kannywood
Samu kari