Allah ya yarda, Tsohuwar jaruma Saima Muhammad ta amarce

Allah ya yarda, Tsohuwar jaruma Saima Muhammad ta amarce

  • A ranakun karshen makon jiya ne labarai suka fara yawo kan auren sirri da jaruma Saima Muhammad ta yi
  • Kyakyawar jarumar kuma mai kyan jiki ta dade tana jan zarenta a masanaantar saboda ta kwashe sama da shekaru 23 tana fim
  • Abokan aikinta sun dinga wallafa hotunanta tare da taya ta murnar wannan abun alkhairi da ya faru da ita duk da babu bayani kan wanda ta aura

Kamar yadda ya zama yayi a halin yanzu ga 'yan fim, kwatsam aka ji labarin auren jaruma Saima Muhammad wanda ta yi a karshen makon jiya.

An ga abokan aikinta suna ta wallafa hotunan ta suna taya murnar auren ba tare da cikakken bayanin wanda ta aura ko inda aka yi auren da sauran makamantan bayanai ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Allah ya yarda, Tsohuwar jaruma Saima Muhammad ta amarce
Allah ya yarda, Tsohuwar jaruma Saima Muhammad ta amarce. Hoto daga @rashidamaisaa
Asali: Instagram

Saima Muhammad jaruma ce da ta taka rawar gani a masana'antar Kannywood sama da shekara 23 da suka gabata wanda a kiyasi an tabbatar da cewa babu wata mace sa'ar ta a masana'antar in banda irinsu Mama Tambaya.

Amma daukacin wadanda suka yi zamani tare a farkon zuwan ta sun rasu, wasu sun yi aure sun hayayyafa sai kuma wadanda suka ajiye sana'ar ko maza wadanda ta zo ta tarar ake cigaba da damawa da su kamar su Shehu Hassan Kano, Ibrahim Mandawari, Hamisu Iyantama da sauran wadanda a yanzu duk dattijai suke fitowa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumar Allah ya ba ta kyan jikin da kowa ke magana inda har Ibrahim Mandawari a lokacin baya yake mata kirari da Benu ba kya tsufa, sai dai ki sake sabon gashi.

Hakan yasa jarumar har yanzu take sajewa a cikin 'yan matan Kannywood irinsu Hadiza Gabon, Halima Atete, Hauwa Waraka, Jamila Nagudu da sauransu.

Kara karanta wannan

Ina Matukar Buƙatar Aure: Ɗan Najeriya Ya Koka Tare Da Wallafa Bidiyon Ɗakinsa Da Kaya a Hargitse

Allah ya basu zaman lafiya da albarkar aure tare da mijinta.

Zafafan hotunan wankan da Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar Maishadda ta dauka a wurin bikinsa

A wani labari na daban, a yayin shagalin bikin Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da Hassana Muhammad, jarumai, mawaka da dukkan 'yan masana'antar sun samu halarta, hakan yasa aka yi bikin a fili domin dakin taro ba dole ya dauke su ba.

'Yan fim abokan sana'arsu sun matukar yi musu kara inda suka fito kwan su da kwarkwatarsu suka halarci bikin.

Manya irinsu Ali Nuhu, Rarara, Adam Zango duk sun halarta, kai hatta manyan mata irinsu Saratu Gidado, Hadizan Saima, Teema Makamashi duk sun samu halartar wurin bikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel