Mawakin Buhari, Rarara ya gwangwaje Furodusa Maishadda da dalleliyar Mota

Mawakin Buhari, Rarara ya gwangwaje Furodusa Maishadda da dalleliyar Mota

  • Fitaccen mawakin shugaba Buhari, Dauda Kahutu Rarara, ya gwangwaje Furodusa Abba Abubakar Mai Shadda da zukekiyar mota
  • Furodusa Mai Shadda da kansa ya bayyana hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram a ranar Talata
  • Ya mika tarin godiyarsa tare da fatan alheri ga Rarara wanda ya kira da Babban Yaya inda ya saka hotunan motar kirar Honda

Kano - Fitaccen mawakin siyasan nan, Dauda Kahutu Rarara, ya bai wa furodusa Abba Abubakar Mai Shadda kyautar dalleliyar mota kirar Honda.

A wata wallafa da furodusa Mai Shadda ya fitar a shafinsa na Instagram @realabbamaishadda a ranar Talata, ya mika matukar godiyarsa ga mawakin tare da wallafa hotonsu tare da kuma na zukekiyar motar da ya gwangwaje shi da ita.

Mawaki Rarara ya gwangwaje Furodusa Abba Maishadda da tsaleliyar Mota
Mawaki Rarara ya gwangwaje Furodusa Abba Maishadda da tsaleliyar Mota. Hoto daga @realabbamaishadda
Asali: Instagram
Ga abinda wallafar ta kunsa: "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. Ina matukar mika godiya ga babban yaya @rarara_fc. Allah ya saka da gidan Aljannah

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

"Ka yi mun komai a rayuwata, kuma kana kan yi mun komai. Allah ya kare ka daga dukkanin sharrin mutum da aljan.
"Allah ya kara bunkasa arzikin ka. Allah ya kara maka nasibi da daukaka. Allah ya kara sanya albarka a cikin rayuwarka. Ameen summa Ameen."

Sanannen abu ne cewa mawakin ya yi shuhura ne tun lokacin zaben 2015 inda ya dinga yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wakoki na kamfen masu matukar kayatarwa.

Ya cigaba da tashe har zuwa 2019 inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kamfen din zarcewa mulkin Najeriya.

Makusantan mawakin, 'yan uwa da abokan arziki har da abokan sana'a suna yawan bayyana yadda yake gwangwaje su da kyautar girma.

Zafafan Hotunan kafin aure na jaruma Hassana Muh'd da Furodusa Maishadda sun bayyana

Kara karanta wannan

Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa

A wani labari na daban, kyawawan hotunan furosuda Abubakar Bashir Maishadda tare da amaryarsa jaruma Hassana Muhammad sun bayyana ana sauran kwanaki kalilan bikin masoyan.

Tun dai a karshen watan Fabrairu aka bayyana cewa furodusa Maishadda zai angwance da maasoyiyarsa Hassana Muhammad kuma katin bikin ya karade kafafen sada zumunta ta Instagram.

A safiyar yau Laraba ne jaruma Hassana Muhammad ta wallafa kyawawan hotunanta tare da angonta wanda suka sha kyau ba kadan ba.

Jama'a da dama sun dinga taya su murnar wannan abun farin ciki da zai same su cikin kwanaki kadan masu zuwa, inda masoyansu suke cigaba da yi musu Allah sam barka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng