Manyan jaruman kannywood maza 4 da suka shafe sama da shekaru 20 suna fim kuma ake yi da su har yau

Manyan jaruman kannywood maza 4 da suka shafe sama da shekaru 20 suna fim kuma ake yi da su har yau

Kannywood masana’anta ce ta shirya fina-finan Hausa mai daddadiyar tarihi a yankin arewacin Najeriya. An kafa ta tsawon shekaru masu yawa da suka gabata tunma kafin ta samu sunan da take amsawa a yanzu.

Masana’antar fim din tana kuma kunshe ne da manyan jarumai maza da mata da dama.

A wannan rahoto, Legit Hausa ta zakulo wasu manyan jarumai maza hudu wadanda suke harkar fim fiye da shekaru 20 da suka gabata kuma har yau ana damawa da su a masana’antar.

Kusan wadannan jarumai na cikin wadanda suka jajirce wajen ganin Kannywood ta kai matsayin da take kai a yanzu.

Manyan jaruman kannywood maza 4 da suka shafe sama da shekaru 20 suna fim kuma ake yi da su har yau
Manyan jaruman kannywood maza 4 da suka shafe sama da shekaru 20 suna fim kuma ake yi da su har yau Hoto: Uzomedia TV/ Instagram/yakubu_mohammed_backup/sarkin_dai_ali_nuhu
Asali: UGC

Ga jerin jaruman a kasa:

Kara karanta wannan

Kannywood: Wasu Shahararrun Jarumai Mata Da Aurensu Ya Mutu

1. Ali Nuhu

An haifi jarumi Ali Nuhu Mohammed wanda aka fi sani da ‘Sarki mai Kannywood’ a ranar 15 ga watan Maris, 1974.

Ali Nuhu ya kasance daya daga cikin manyan jarumai maza da tauraronsu ta fara haskawa tun a 1999 kuma ya samu karbuwa sosai bayan rawar ganin da ya taka cikin fim din Sangaya wanda shine kusan lamba ta daya a zamanin.

Ali ya yi fina-finai da yawa sannan kuma ya sha karbar lambar yabo a matsayin jarumin jarumai na masana’antar. Yana kuma da kamfaninsa mai suna FKD Production.

Wani abun mamaki shine tsawon shekarun nan da ya shafe a masana’antar, tauraronsa bai taba yin kasa ba domin har gobe yana cikin masu fada aji da ake ji da su a Kannywood.

2. Sani Musa Danja

An haifi Sani Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Sani Danja a ranar 20 ga watan Afrilun 1973.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Sani Danja ya shiga masana’antar fim din da kafar dama a shekarar 1999 inda ya fara fitowa a cikin wani fim mai suna ‘Dalibai. Yana daya daga cikin manyan jaruman da ake ji da su a lokacin saboda kasancewarsa gwanin iya rawa.

Jarumin yana daya daga cikin jaruman da suka jajirce tare da taka rawar gani wajen daukaka tukar masana'antar. Kuma har gobe ana damawa da shi cikin masu fada a ji sannan yana da kamfaninsa mai suna '2 Effects' wanda suke ja tare da aminsa Yakubu Muhammad.

3. Yakubu Muhammad

An haifi jarumi Yakubu Muhammad a ranar 25 ga watan Maris 1973. Ya shiga masa’antar Kannywood a 1998 a matsayin marubuci a bayan fage.

Hakazalika, Yakubu Muhammad mawaki ne sannan bayan wasu shekaru a masana’antar sai ya fara bayyana a matsayin jarumi cikin fina-finai inda ya fito a fim dinsa na farko mai suna ‘Gabar Cikin Gida’ tare da amininsa Sani Danja.

Kara karanta wannan

Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000

Tun daga lokacin sai ya fara fitowa a matsayin jarumi cikin fina-finai kuma har gobe tauraronsa na haskawa a masana’antar ta Kannywood.

4. Abubakar Baballe Hayatu

An Haifi Abubakar Baballe Hayatu wanda aka fi sani da Baballe Hayatu a ranar 11 ga watan Agustan 1975.

Baballe yana daya daga cikin tsoffin jarumai maza a masana’antar Kannywood kuma ya fara fim ne tun zamanin su Ali Nuhu. Ya fito a fina-finai irin su ‘Abin Sirrine, Aya Tawakkali, Furuci, Mashi, Mujadala, Gyale, Biki Budiri da sauransu.

Har gobe Baballe na fitowa a cikin fina-finai kuma ana damawa da shi sosai a cikin masana’antar.

Yadda na hadu da baturiya na aure ta bayan rabuwa ta da Fati Mohammed, Sani Mai Iska

A wani labari, tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sani Musa Mai Iska ya bayyana cewa ya taba auren wata Baturiya mai suna Sarah.

Mai Iska ya ce sabanin yadda ake fadi cewa haduwarsu da ita ne yasa ya rabu da Fati, ya hadu da Sarah ne a kasar Ingila bayan ita Fatin ta dawo gida.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda hudu har lahira

Ya ce sun hadu da baturiyar ne a watan Ramadana ta sanadiyar wani taimako da ta nema daga gare shi na ya bata makwanci ana ruwan sama, ita kuma bakuwa ce daga birnin Boston.

Asali: Legit.ng

Online view pixel