Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000

Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000

Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, tana daddiyar tarihi a kasar Hausa, kuma ba za a taba bayar da wannan tarihi ba tare da an ambaci sunayen wasu tsoffin jarumai mata da suka zamo madubin dubawa ga masu tasowa ba.

Duk da cewar babu ingantattun kayan aiki na zamani a wancan lokaci, wadannan jarumai sun jajirce tare da taimakawa matuka wajen daukaka sunan masana’antar har ta kai inda take a yanzu.

A wannan zaure, Legit Hausa ta zakulo maku wasu manyan jarumai mata 5 da tauraronsu ya haska sosai a duniyar fina-finan Hausa cikin shekara ta 2000.

Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000
Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000 Hoto: NAIJASTICK/Twitter/@RDawayya/HUTUDOLE/Opera News
Asali: UGC

Jaruman sune kamar haka:

1. Fati Mohammad

Fati Muhammad ta kasance manyan jaruman fim mata da tauraruwarsu ta haska sosai a zamanin baya. Jarumar mai shekaru 39 ta fito ne daga kabilar Fulani na jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Hasashe mai daukar hankali: Musulmai za su azumci Ramadana sau biyu a 2030

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An haifeta a Kano kuma ta taso a jihar inda ta shiga harkar fim tun tana da shekaru 16 a duniya ta sanadiyar shahararren jarumi kuma mai shirya fina-finai, Tahir Muhammad Fagge.

Ta taka rawar gani a wasu tsoffin fina-finai irin su; Sangaya, Da Babu, Marainiya, Zarge, Tangarda, Tawakkali, Garwashi, Kudiri and Samodara.

Ta kuma yi suna sosai a cikin fim din Sangaya wanda suka yi soyayya da jarumi Ali Nuhu wanda ya fito a matsayin dan sarki a cikin wasan.

Jarumar ta kuma auri abokin sana’arta, Sani Musa Mai Iska inda suka yi rayuwar aurensu a kasar Ingila har dai Allah ya kawo rabuwarsu.

2. Abida Muhammad

Abida Muhammad ta kasance shahararriyar tsohuwar jaruma a masana’antar ta Kannywood wacce suka yi tashe a lokaci daya da Fati sannan sun kasance aminan juna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

Jarumar ta yi tashe sosai a cikin shekarar 2000 saboda iya fim dinta gashi ita din gwanar iya rawa ce a lokacin. Ta yi suna sosai a cikin fim din Sangandale da ta yi tare da manyan jarumai irin su Ali Nuhu, Marigayi Ahmad S Nuhu da Fati Muhammad.

Ta kuma fito a fim din Mujadala na kamfanin FKD wanda ya samu karbuwa sosai a kasar Hausa a zamanin. Ta kuma fito a fina-finai irin su Badali, Kauna, Ukuba, da Furuci.

Abida ta bar harkar fim ne bayan ta yi aure sannan mijinta ya rasu amma ta sake aure a shekarar 2018.

3. Rukayya Dawayya

Jarumar mai shekaru 37 ta kasance haifaffiyar jihar Kano kuma ta shiga harkar fim tun tana matashiyar budurwa mai shekaru 15 inda ta yi suna a cikin fim dinta mai suna Dawayya a 2000.

Wasu daga cikin fina-finai da ta yi sun hada da Gidauniya, Sarauniyar Kyau, Hajjaju, Kun Yi Sake, Ta Isa, Ta Fi Su, Halimatus Sadiya, Hawan Hawa, Zahra’u, Zato Ne, Nawwara, da Ummi Sambo.

Kara karanta wannan

Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

Jarumar ta yi aure a shekarar 2013 amma suka rabu da mijin daga baya bayan Allah ya albarkace su da haihuwar da namiji. Bayan nan ta dawo harkar fim sannan tana da kamfaninta na fim mai suna Dawayya movies.

4. Balaraba Muhammad

A watan Maris 2022, Allah ya yiwa shahararriyar jaruma Balaraba Mohammed rasuwa sakamakon hatsarin mota bayan ta auri abokin sana’arta Shuaibu Lawal da aka fi sani da Kumurci.

Mutuwar jarumar ya girgiza masana’antar shirya fina-finan dama masu kallon wasannin.

Kafin mutuwarta, Balaraba ta kasance tauraruwa wacce ta yi suna sosai a duniyar fim cikin dan kankanin lokaci saboda salon iya fim dinta da kuma tsantsar kyawu da Allah ya yi mata.

Ta yi fina-finai irin su Maryam, Tawakkali, Furuci, Hali, Jaheed, So, Biyayya, Yakini, Tasiri, Miras, Burin-zuciya, Matausaya, Sarkakiya, Harsashe, Sababi, Fata-nagari, Kacibus, Nabila, Amalala, Buri da Qauli.

5. Hauwa Ali Dodo

Marigayiya Hauwa Ali Dodo wacce aka fi sani da Biba Problem ta kasance babbar jaruma a masana’antar Kannywood a lokacin da aka fara kafa ta. Ta yi suna sosai a cikin fim din ‘Ki yarda da ni’.

Kara karanta wannan

Mari mai kwance kunne: Sabon bidiyo ya nuna yadda matar Obiano ta takali fadan Bianca Ojukwu

Jarumar ta kasance cikin jarumai da suka yi tashe sosai kuma mutum ce bai iya magana a tarihin masana’antar wacce ta shafe tsawon shekaru 20 tana fim kafin mutuwarta. Ta yi fim irin su Sangaya, Zarge, Daskin Da Ridi, da sauransu.

Ta rasu a mummunan hatsarin mota a hanyarta ta zuwa Kaduna daga Jos a 2010.

Gaskiyar abun da ya raba aurena da Fati Mohd – Sani Musa Mai Iska

A gefe guda, tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa kuma miji ga tsohuwar jaruma, Fati Muhammad, Sani Musa Mai Iska ya magantu a kan abun da ya kawo rabuwar aurensu a shekarun baya.

Mai Iska ya tuno yadda aurensu ta kasance da Fati wacce suka lula suka bar kasar zuwa Ingila yan watanni bayan bikin nasu sakamakon samun damar shiga wani shiri na wayar da kai kan Kanjamau da ita jarumar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel