Hotunan jaruma Nafisa Abdullahi yayin da ta je Umra, ta bayyana muhimmin abinda ta roki Allah

Hotunan jaruma Nafisa Abdullahi yayin da ta je Umra, ta bayyana muhimmin abinda ta roki Allah

  • Kyawawan hotunan jaruma Nafisa Abdullahi yayin da ta kai ziyara Makka don yin Umrah sun bayyana
  • Jarumar ta sanar da yadda a koda yaushe ta je Ka'aba take addu'ar Allah ya sake mayar da ita a wani lokaci
  • Ta mika godiyarta ga Allah madaukakin Sarki da ya ke amsa mata addu'o'inta inda yake sake mayar da ita dakin kasar

Makka, Saudi Arabia - Kyawawan hotunan fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, yayin da ta ziyarci garin Makka domin yin Umrah sun bayyana.

Jarumar ta wallafa hotunan a shafinta na Instagram inda ta bayyana sanye da bakar doguwar riga wacce ta fito da matukar kyan ta.

A hotunan da ta wallafa, an hango Larabawa tare da hoton dakin Ka'aba wanda ke da dan nisa da inda ta tsaya ta dauka hotunan nata.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala yayi watsi da lauyansa a kotu, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su

Hotunan jaruma Nafisa Abdullahi yayin da ta je Umra, ta bayyana muhimmin abinda ta roki Allah
Hotunan jaruma Nafisa Abdullahi yayin da ta je Umra, ta bayyana muhimmin abinda ta roki Allah. hoto daga @nafeesat_official
Asali: Instagram

Ba hotunan ko zuwa umrah bane ya dauka hankalin jama'a, rubutun da ta yi a kasan hotunan ne suka dauki hankali kuma suka janyo mata tsokaci masu kyau daga masoyanta da mabiyan shafinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wallafar da tayi a kasan hotunan, ta ce:

"Addu'ar farko da nake yi a duk lokacin da na zo nan shi ne Allah ya sanya min albarka kuma ya bani damar sake dawowa.
"A koda yaushe ana amsa min addu'o'i na. Godiya ta tabbata ga Allah."

Jama'a sun yi martani

Babu bata lokaci masoya da mabiya shafin jarumar suka fara tsokaci. Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a:

@kabiru.ibrahim cewa ya yi: "Mu ma a yi mana addu'a Allah ya kaimu muma"
@ig_kuda ya ce: "Masha Allah, Allah nake fatan ya kasnace tare da ke a yanzu da ko yaushe sarauniyata daya tak a duniya."

Kara karanta wannan

Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa

@ummuumarzakaria ta ce: "Allah ya kira ni, albarkan Annabi SAW. Ameen."

Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka

A wani labari na daban, kamar yadda Legit.ng ta gano, batun da yafi yi wa 'yan Kannywood zafi a maganar sarkin waka shi ne batun lalata da mata kafin a saka su a fim inda matan Kannywood ke ta fitowa suna musanta waccan maganar da yayi.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta rubuta budaddiyar wasika cikin harshen turanci a shafinta na Instagram kuma ta kara da bayani a kasan wasikar da harshen Hausa inda ta bayyana cewa babban zargi ya fitar tunda ta na cikin matan masana'antar.

Jarumar ta yi kira ga sarkin wakan idan ya na da matsala da wani ne, ya bayyana sunansa su yi ta kare ba wai ya bata masana'antar ba baki daya.

Har ila yau, a zancenta cikin budaddiyar wasikar, ta yi kira ga matan masana'antar kan cewa duk wacce darakta ko furodusa ya taba nemanta da lalata, ta fito ta bayyana sunansa domin a magance matsalar.

Kara karanta wannan

Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi

Asali: Legit.ng

Online view pixel