Yadda na hadu da baturiya na aure ta bayan rabuwa ta da Fati Mohammed, Sani Mai Iska

Yadda na hadu da baturiya na aure ta bayan rabuwa ta da Fati Mohammed, Sani Mai Iska

  • Sani Musa Mai Iska ya ce ko shakka babu ya hadu da baturiya a zaman da ya yi a kasar Ingila harma aure ya kullu a tsakaninsu
  • Sai dai ya ce ba saboda ita ya rabu da Fati Mohammad ba domin basu hadu da Sarah ba har sai bayan da jarumar fim din ta dawo gida Najeriya
  • Tsohon jarumin na Kannywood ya kuma ce ya rabu da Sarah bayan sun yi zaman aure na watanni uku saboda akwai cutuwa a zamanta a Najeriya

Tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sani Musa Mai Iska ya bayyana cewa ya taba auren wata Baturiya mai suna Sarah.

Mai Iska ya ce sabanin yadda ake fadi cewa haduwarsu da ita ne yasa ya rabu da Fati, ya hadu da Sarah ne a kasar Ingila bayan ita Fatin ta dawo gida.

Kara karanta wannan

Gaskiyar abun da ya raba aurena da Fati Mohd – Sani Musa Mai Iska

Ya ce sun hadu da baturiyar ne a watan Ramadana ta sanadiyar wani taimako da ta nema daga gare shi na ya bata makwanci ana ruwan sama, ita kuma bakuwa ce daga birnin Boston.

Yadda na hadu da baturiya na aure ta bayan rabuwa ta da Fati Mohammed, Sani Mai Iska
Yadda na hadu da baturiya na aure ta bayan rabuwa ta da Fati Mohammed, Sani Mai Iska Hoto: NAIJASTICK/BBC Hausa
Asali: UGC

Da aka tambaye shi a shirin BBC Hausa na ‘daga bakin mai ita’ kan rade-radin da ake ta yi cewa ya samu wata baturiya ne shiyasa ya rabu da Fati, sai Sani ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Eh akwai baturiya amma ita sai bayan da Fati ta dawo ne muka hadu, ita kuma mun hadu da ita ne kan wani dalili.
“Sunanta Sarah, garinsu shine Boston. Mun hadu da ita da azumi zan tafi masallaci da daddare, goman karshe, ana ruwa saboda haka sai na same ta ‘city centre’ a tashar mota a zaune tana ganin mota sai ta tashi tsaye sai ta tsayar dani, sai na tsaya sai ta bude kofa sai ta ce na bata gudunmawa, ita bakuwa ce daga Boston ta ita abokanta amma sun bace mata kuma dare ya yi.

Kara karanta wannan

Bana yi kuma: Budurwa ta soke aurenta ana saura kwana 3 saboda sun samu sabani da angon nata

“Sai nace toh shikenan ai abu mai sauki ne zan iya kai ki wajen yan sanda ko kuma otel idan ya so gobe sai ki nemi hanyar gida, sai ta ce a’a ita dai idan zan yarda na kaita nawa gidan ta kwana ya fi sauki. Sai nace me yasa sai tace saboda idan na magana ta je wajen yan sanda mahaifiyarta ta samu labari ranta zai baci, sai nace toh, sai na kaita gidanmu da gari ya waye sai muka je gidansu, muka gaisa da mahaifiyarta ta bani labarin komai da komai, toh daga nan muka fara.
“Sai mahaifiyarta ta zo gidana wani lokaci, ta ce ta ji labarin cewa Sarah zata bini Najeriya, nace eh gaskiya ne, kuma ta ce za ku yi aure, nace eh gaskiya ne, kuma za ta musulunta, nace eh gaskiya ne.
“Da na dawo gida Najeriya da kamar wata biyu zuwa uku, sais u kuma suka zo, muka zo aka daura mana aure a ranar wani Juma’a. Da baki daya watan ta uku sai kuma ni na hangi akwai cutarwa a zamanta a Najeriya saboda yanayin zafi da wasu abubuwa kuma Allah ya yi mata tana da garin jiki, toh sai na dan yi mata siyasa nace kin ga abun da ya kamata, nan ba kamar can ba, saboda haka ki koma gida, bayan ta koma gida muka dan samu hutu haka aka dan yi shekara ko watanni haka sai mu yanke abun yi.

Kara karanta wannan

Mijin Status: Yadda budurwa ta ga saurayi a WhatsApp, ta san yadda ta aure shi

“Mun rabu a kan wannan sai ita ta koma gida ni kuma ina Najeriya. Sai nace mata toh gaskiya Sarah yanzu damar ki ce kina gida ni kuma ina nan Najeriya meye burinki, sai tace burinta tana so ta haihu, sai nace maslaha ita ce zan sake ki.”

Gaskiyar abun da ya raba aurena da Fati Mohd – Sani Musa Mai Iska

A gefe guda, tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa kuma miji ga tsohuwar jaruma, Fati Muhammad, Sani Musa Mai Iska ya magantu a kan abun da ya kawo rabuwar aurensu a shekarun baya.

Mai Iska ya tuno yadda aurensu ta kasance da Fati wacce suka lula suka bar kasar zuwa Ingila yan watanni bayan bikin nasu sakamakon samun damar shiga wani shiri na wayar da kai kan Kanjamau da ita jarumar ta yi.

Jarumin ya ce bayan sun je kasar Ingila sun kammala shirin, sai suka dawo gida Najeriya amma sai shi ya sake komawa kasar saboda wani dalili nasa na gashin kansa. Ana haka sai ya ga cewa zai fi samun nutsuwa idan matarsa na kusa da shi don haka ya nemi Fati ta dawo kasar ita ma.

Kara karanta wannan

Dan baiwa: Bidiyon mai shekaru 8 da ya haddace Al-Qur'ani da wasu littatafai a Zaria

Asali: Legit.ng

Online view pixel