Dandalin Kannywood
Bayan kusan shekaru ashirin da rasuwar rabin ransa, jaruma Balaraba Muhammad, jarumi Shu'aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya sake angwancewa da budurwa.
Batun Ladin Cima na ci gaba da tayar da kura a masana'antar Kannywood, a yanzu haka jarumi Nuhu Abdullahi ya caccaki Naziru Ahmad kan yiwa lamarin kudin goro.
Mahaifiyar mai jegon tayi fitar kece raini inda ta saka wani tsadajjen leshi dan ubansu da sarkar gwal da aka yi kiyasin kudin ta ya kai naira miliyan sha daya.
Mutane a shafukan sada zumunta sun dinga maganganu daban-daban kan ikirarin jaruma Ladin Cima na cewa wasu furdusoshi na biyan ta dubu biyu zuwa dubu biyar.
Furodusan masana’antar Kannywood, Nazir Adam Salihi, ya karyatu batun da jaruma Ladin Cima ta yi cewa ba a taba biyan ta kudi masu yawa ba a fitowar da take yi.
Jaruma Ladin Cima Haruna ta ce ta soma harkar fim bayan rasuwar mijinta inda ta ce dama tun a baya tana da sha'awar fim din. Ta ce Kaduna suke zuwa su yi fim.
Abdul Saheer ya bada labarin yadda Ali Nuhu ya ga mai tallar awara ta yi bari,ya dauko kudin da yayi aiko ko aljihu bai saka ba ya bata kyauta,yace ta bar kuka.
Wani ma'abocin amffani da kafar sada zumunta ta Twitter mai suna Babayo ya yi wa jaruma Hadiza Gabon zagin cin mutunci ta sashin sako amma ta yi masa addu'a.
Jarumin masana’antar Kannywood, Isa A Isa, ya yi martani a kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna, ya ce Allah ne ya tabbatar da gaskiya a kan lamarinsu.
Dandalin Kannywood
Samu kari