Cristiano Ronaldo
A yayin da shekarar 2020 ke karato wa gadan-gadan, babbar kafar watsa labaran kwallon kafa ta Duniya, Goal.com, ta yanke shawarar fayyace gwarazan 'yan kwallo da suka yi fice ta fuskar kwazo a tsawon shekaru 10 da suka gabata.
Ronaldo ya shiga littafin tarihi bayan ya ci kwallo 700 a ban kasa. Yanzu Ronaldo ya shiga sahun manyan ‘yan kwallon Duniya irin su 805: Bican 772: Romario 767: Pele 746: Puskas 735: Muller 700.
Cristiano Ronaldo ya fadi lokacin da zai yi ritaya daga buga kwallon kafa. Tauraron Duniya Ronaldo ya hararo karshensa ne a kwallo nan da ‘dan lokaci ba da yawa ba wanda hakan ya ba kowa mamaki.
Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka a gaban Duniya wajen wata hira inda Tauraron Duniyar ya fadi babban abin da ke masa ciwo. Abin da ya sa ‘Dan wasa Ronaldo kuka zai ba ka tausayi sosai.
Jiya da dare Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 4 a wasan Portugal da Lithuania. Ronaldo ya dirkawa kasar Lithuania kwallaye 4 a raga shi kadai inda kasarsa ta samu nasara da ci 5-1.
Ronaldo da Messi wanda tun daga 2018 zuwa yanzu, da su ake damawa a kwallo za su yi abin da ba a taba gani ba bayan Cristiano Ronaldo ya yi wa Messi tayin zaman cin tuwon dare.
Idan mu ka koma kwallo, za mu ji cewa Cristiano ya na ganin cewa ya fi Messi. Babban ‘Dan kwallon na Duniya ya ce ya zagaya kungiyoyi da dama ya dauki kofi wanda ta na ya sha ban-ban da Messi.
Hukumar FIFA ta ce a halin yanzu kofar fara jefa kuri'u a bude take domin tantance gwarzon bana. 'Yan wasa, masu horaswa wato koci, masoya da kuma 'yan jaridu na kwallon kafa su ne za su tantance gwarzon bana.
Mun kawo maku jerin manyan ‘Yan kwallon da su ka fi kowa albashi a Duniya. ‘Yan kwallo 3 ne su ka shiga cikin mutane 100 da Forbes ta bayyana na wadanda su ka samu makudan kudi a bana.
Cristiano Ronaldo
Samu kari