Roberto Carlos: 'Daki guda mu ka rika amfani da shi da Ronaldo De Lima

Roberto Carlos: 'Daki guda mu ka rika amfani da shi da Ronaldo De Lima

Tsohon ‘dan wasan nan na kasar Brazil da ya bugawa Real Madrid, Roberto Carlos ya bada labarin irin alakarsa da Abokin wasansa a lokacin da su ke buga kwallo, Ronaldo de Lima'.

Roberto Carlos ya ke cewa ya kwanta barci a daki daya da Ronaldo fiye da yadda ya kwanta da Mai dakinsa a Duniya. Carlos yace ya fara haduwa da Ronaldo ne tun a shekarar 1993.

“Na hadu da Ronaldo ne a 1993 kuma tun daga wannan lokaci, daki daya mu ke amfani da shi. Na yi barci tare da Ronaldo fiye da yadda na kwanta barci da Mai dakina.” Inji Carlos.

Tsohon ‘dan wasan bayan na Real Madrid mai shekara 46 a Duniya ya fadawa Jaridar 90mins wannan ne kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Litinin 14 ga Watan Oktoban 2019.

Ronaldo da Roberto Carlos su na cikin wadanda su ka kai Brazil ga nasara a gasar cin kofin Duniya a 2002 wanda aka yi a Koriya da Jafan. Ronaldo ya zuba kwallaye rututu a Gasar.

KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ya zura kwallonsa na 700 a Duniya

A game da tsohon Kocinsa a Real Madrid, Vicente Del Bosque, Carlos ya na cewa: “Kusan Abokinmu ne. Ba mu bukatar wasu dokoki. Mun san duk abin da yake bukata sarai.”

“A Ranar Litinin, a kan fara atisaye karfe 5:00 na rana. Wani lokacin haka Talata. (Del Bosque) bai cewa mu zo fili tun karfe 11:00 na safe domin maganar gaskiya, babu wanda zai zo.

A 1993 lokacin da Ronaldo ya fara kwallo, ya na da shekara 17. Ronaldo ya fara wasa ne a Cruziero inda a wasan farkonsa ya ci kwallaye biyar. A kakar 2002 Ronaldo ya hadu da Carlos a Sifen.

Bayan Real Madrid inda ‘dan kwallon ya shafe shekara da shekaru, Ronaldo De Lima’ yana tare da Roberto Carlos a gida inda su ka taimakawa kasar Brazil wajen lashe kofofi a Duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel