Abubuwa 9 da suka sha gaban Messi a yanzu

Abubuwa 9 da suka sha gaban Messi a yanzu

A makon nan ne kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya karbi kyautar takalmin zinare karo na shida, bayan jefa adadin kwallaye mafi yawa tsakanin takwarorinsa dake manyan gasannin nahiyyar Turai.

Wannan shi ne karo na uku kenan da Messi ya lashe kyautar takalmin zinaren bayan da ya lashe kyautar a shekarun 2010, 2012 da kuma 2013. Hakan ya ba shi damar zarta abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo da takalman zinaren biyu, wanda ya lashe kyautar sau hudu.

Gwarzon dan kwallon kafa da ya shahara a doron kasa, ya yi bajinta da dama a fagen taka leda a duniya da za a dade ba 'a manta da shi ba.

Sai dai duk da wannan bajinta da Messi ya yi a fagen tamaula, akwai wasu kalubale da suka sha gabansa wanda jaridar BBC Hausa ta wallafa a rahoton ranar 16 ga watan Oktoban da muke ciki.

Ga jerin kalubalai 9 da suka sha gaban Messi a yanzu:

1. Tarihin yawan buga wa Barcelona wasanni.

Bayan buga wa kungiyar Barcelona wasanni 692, a yanzu Messi shi ne na biyu a jerin 'yan wasa da suka fi buga wa kungiyar wasanni masu yawa, wanda ya kasance na daya shi ne Xavi Hernandez, wanda ya buga wasanni 767.

2. Takalmin zinare na bakwai a gasar La Liga da gasannin nahiyyar Turai.

Bayan lashe kyautar cin kwallaye mafi yawa a gasar La Liga da kuma gasannin nahiyyar Turai karo shida, Messi ya na fatan sake lashe takalmin zinare na bakwai a matsayin dan wasan da ya fi jefa kwallaye a koma.

3. Yawan lashe kofuna

A halin yanzu tsohon dan wasan Manchester United, Ryan Giggs da kuma tsohon mai tsaron raga kungiyar Barcelon da Porto, Vitor Baia, sun sha gaban Messi a matsayin 'yan wasan tamaula da suka fi kowa lashe kofuna. Sai dai da zarar kungiyar Barcelon ta lashe wasu kofuna uku nan gaba, shikenan Messi zai kasance marikin kambun dan wasan a yafi takwarorinsa lashe kofuna.

4. Lashe kofin zakarun turai biyar

Idan har Barcelona ta lashe wata gasar kofin zakarun nahiyyar Turai a nan gaba, Messi zai daga na biyar jimilla kenan bayan lashe wasu hudun a baya.

5. Yawan buga wa Barcelona wasan hammaya na El Clasico

A halin yanzu, tsohon dan wasan Barcelona, Xavi Hernandez, shi ke rike da tarhin yawan buga wa Barcelona wasan hamayya a tsakaninta da Real Madrid wanda ake yi wa lakabi da El Clasico, sai dai Messi wanda ya yi karawa 41, idan ya buga wanda za a yi ranar 26 ga watan Oktoba zai yi kan-kan-kan da na Hernandez.

'Yan kwallon Real Madrid uku sun buga wasan El Clasico 42 daidai da na Xavi, inda Sergio Ramos har yanzu ke buga wasannin daga cikin sauran.

6. Jefa kwallo sau 50 daga damar bugun tazara mai 'yanci

Kawo wa yanzu, Messi ya ci kwallaye 49 daga bugun tazara, inda yana da kwallaye 43 a Barcelona da kuma 6 a tawagar kasar sa ta Argentina.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta koka kan lalacewar manyan hanyoyin gwamnatin tarayya

7. Cin kwallo uku rigis a wasa daya daga bugun tazara

A karo da dama Messi ya ci kwallo biyu daga bugun tazara, idan har zai samu damar cin uku a wasa guda, tabbas hakan zai daukaka darajarsa a idon masoya da za su samu abun fade.

8. Cin kwallo 500 a gasar kasa wato League

Kyaftin din Argentina ya haura 400 da ya zura a raga a bara, kawo yanzu ya ci 420 a La Liga. Wanda ya sha gabansa a yanzu shi ne Josef Bican da ya jefa kwallo 447, sai kuma Uwe Seeler mai guda 444 a raga.

9. Cin kwallo 700

A halin yanzu Messi yana da jimillar kwallo 672 a fagen tamaula, guda 604 ya jefa wa kungiyar Barcelona da 68 a tawagar Argentina, hakan yana nufin dan wasan yana daf da kai wa 700 kenan muddin rai da lafiya ba su taka mai burki ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel