‘Dan wasa Ronaldo ya kamo tarihin Trezeguet a wasan Fiorentina

‘Dan wasa Ronaldo ya kamo tarihin Trezeguet a wasan Fiorentina

Tauraron Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa na tara a jere a gasar Seria A na kasar Italiya a Ranar Lahadi, 2 ga Watan Fubrairun 2020.

‘Dan wasan gaba Ronaldo ya zura kwallaye biyu a wasan Fiorentina da Juventus wanda aka buga a filin Old Lady a karshen makon nan.

An tashi wasan 3-0 ne a sakamakon kwallaye biyu da Cristiano Ronaldo ya ci. Daf da za a tashi kuma Matthijs de Ligt ya zura ta uku.

Da wannan nasara da kungiyar Juventus da Ronaldo su ka samu, an kamo tarihin tsohon ‘Dan wasan gaban kungiyar, David Trezeguet.

David Trezeguet shi ne wanda ya taba yin wasanni tara a jere ya na zuba kwallo a raga. A kakar bana Ronaldo ya maimata irin wannan.

KU KARANTA: 'Dan wasa Ronaldo ya fi kowa yawan Mabiya a shafin Instagram

Trezeguet ya kafa wannan tarihi ne a 2005 lokacin da ya ke tashe a kungiyar. An yi shekara 20 ba a samu wanda ya iya kama kafarsa ba.

A bana ne ‘Dan wasan na kasar Portugal ya ke shekararsa ta biyu a Italiya bayan ya tashi daga kungiyar Real Madrid a kasar Sifen.

Fitaccen ‘Dan wasan gaban ya ci kwallonsa na 50 daga zuwansa Juventus zuwa yanzu. Kafin yanzu ya jefa kwallaye 450 a Madrid.

Gabriel Batistuta shi ne wanda ya bar tarihin shafe wasanni 11 a jere ya na zuba kwallo a raga. Ronaldo ya na da damar rusa wannan tarihi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel