Messi, Ronaldo da sauran 'yan kwallo 9 da suka fi kwazo a shekaru 10 da suka gabata
A yayin da shekarar 2020 ke ci gaba da karato wa gadan-gadan, babbar kafar watsa labaran kwallon kafa ta Duniya, Goal.com, ta yanke shawarar fayyace gwarazan 'yan kwallo da suka yi fice ta fuskar kwazo a tsawon shekaru 10 da suka gabata.
Goal ta zabo tawagar 'yan wasa 11 da suka yi zarra a fagen tamaula cikin shekaru goman da suka shude.
Mawallafan Goal da suka zakulo wannan gwarazan 'yan wasa kwallo sun hadar da; Peter Staunton, Stefan Coerts da Sam Brown. Sun yi zakulen su ne duba da bajintar 'yan wasan a kungiyoyinsu na kwallo daban-daban da kuma kasashensu.
Ga jerin tawagar 'yan wasan 11 tare da kasar da suka fito da kuma kungiyoyin da suke taka wa leda wanda Goal ta tabbatar da kwazonsu kamar haka;
Mai Tsaron Gida:
- Manuel Neuer - Jamus - Bayern Munich
'Yan Wasan Baya:
- Dani Alves - Brazil - PSG
- Raphael Varane - Faransa - Real Madrid
- Sergio Ramos - Spain - Real Madrid
- Marcelo - Brazil - Real Madrid
'Yan Wasan Tsakiya:
- Toni Kroos - Jamus - Real Madrid
- Sergio Busquets - Spain - Barcelona
- David Silva - Spain - Manchester City
KARANTA KUMA: Kasafin Kudin 2020: Majalisar Dattawa ta dakatar da zamanta zuwa ranar 29 ga watan Oktoba
'Yan Wasan Gaba:
- Lionel Messi - Argentina - Barcelona
- Robert Lewandowski - Poland - Bayern Munich
- Cristiano Ronaldo - Portugal - Juventus
Legit.ng ta ruwaito cewa, Cristiano Ronaldo ya jefa kwallo ta 700 a ranar Litinin yayin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a karawar da kasar Portuagl ta yi da Ukraine.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng