‘Dan wasa Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa ta 700 a kwallon kafa a wasan Ukraine

‘Dan wasa Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa ta 700 a kwallon kafa a wasan Ukraine

Duk da kasar Portugal ta sha kashi da ci 1-2 a hannun kasar Ukraine a jiya Litinin 14 ga Watan Oktoba, 2019, babban ‘Dan wasan gaban nan Cristiano Ronaldo ya jefa kwallonsa ta 700 a raga.

Cristiano Ronaldo ya sake shiga cikin littatafan tarihin kwallon kafa bayan ya ci kwallonsa na 700. Kawo yanzu dai babu wani mai wasa a Duniya da yake da irin wannan tarin kwallaye.

Mai bin Ronaldo a baya a wannan sahu shi ne Abokin hammayarsa, Lionel Messi na Barcelona. Messi ya na da kwallaye 672 yanzu a Duniya kuma bai nuna wani alamun kakkautawa.

‘Yan wasa irin su Pele da Bican da Romario da Puskas da Muller ne kurum su ka taba cin kwallo fiye da 700 a Duniya. Duka wadannan manyan ‘yan wasa sun yi shekaru da daina buga wasa.

KU KARANTA: Messi ya ce bai ji dadin tashin Ronaldo daga kasar Sifen ba

Wannan na nufin yanzu babu wani ‘dan wasa da ke taka ledan da ya zura kwallaye 700 a raga sai tsohon ‘dan wasan na Manchester United da Real Madrid wanda yanzu ya koma Juventus.

Ronaldo ya ci kwallaye 450 kafin barinsa Real Madrid. Kafin nan ya ci kwallaye sama da 100 a Ingila lokacin da yake wasa a Manchester United. ‘Dan wasan ya kuma ci wa kasarsa kwallo 98.

Daga komawan Ronaldo Juventus zuwa yanzu, ya iya cin kwallaye fiye da 30. Idan aka hada wannan jimilla da abin da ya ci a kungiyar Sporting CP a shekarun baya, ya na da kwallo 700.

Sa’ilin da ya ke kasar Sifen, Ronaldo ya shafe shekaru takwas a jere ya na cin kwallaye fiye da 50. A kakar wasan 2011, sai da babban ‘dan kwallon ya leka raga sau 69 ya kuma dauki kofi a Sifen.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel