Bincike ya bankado cewa kudin da Cristiano Ronaldo yake samu a shafinsa na Instagram yafi wanda yake samu a kulob dinsa na Juventus

Bincike ya bankado cewa kudin da Cristiano Ronaldo yake samu a shafinsa na Instagram yafi wanda yake samu a kulob dinsa na Juventus

- Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na duniya Cristiano Ronaldo bincike ya bankado irin kudin da yake samu a shafinsa na Instagram

- Binciken ya bankado cewa dan wasan na samun kudi a shafinsa na Instagram fiye da yadda yake samu a kulob dinsa na Juventus

- Wannan bincike da aka bankado ya sa Ronaldo ya tserewa abokin hamayyarsa Lionel Messi, inda shi kuma yake daukar kusan rabin abinda Ronaldo din yake dauka

Wani bincike da aka gabatar ya bayyana cewa fitaccen dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo yafi samun kudi a shafinsa na Instagram fiye da yadda kulob dinsa na Juventus ke biyan shi.

Dan wasan mai shekaru 34 a duniya yana samun dala miliyan arba'in da bakwai da digo takwas ($47.8m) daga shafinsa na Instagram, Inda kuma yake samun dala miliyan talatin da hudu ($34m) a kulob din sa na Juventus, kamar yadda Goal.com ta ruwaito.

Bayyanar kudin da dan wasan yake samu a Instagram ya sanya ya doke abokin hamayyarsa Lionel Messi da kuma tauraruwa Kylie Jenner.

KU KARANTA: Fitsararriyar mawakiya Nicky Minaj za ta amarce nan da kwanaki bakwai

Rahoton ya bayyana cewa dan wasan yana samun kimanin dala dubu dari tara da saba'in da biyar ($975,000) a duk tallar da aka sanya a shafin nasa, hakan ya sa ya zama tauraro na farko a duniya da yake samun irin wannan kudin, daga shi sai Kylie Jenner, Selena Gomez da kuma Emily Ratajkowski, haka kuma ya doke abokin hamayyarsa Lionel Messi, wanda yake daukar kusan rabin abinda Ronaldo din yake dauka, wato dala miliyan ashirin da uku da digo uku ($23.3m).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng