Cristiano ya bar tarihi a duniya, yayin da ya zama mutum na farko da yafi kowa mabiya a Instagram a duniya

Cristiano ya bar tarihi a duniya, yayin da ya zama mutum na farko da yafi kowa mabiya a Instagram a duniya

- Cristiano Ronaldo ya bar babban tarihi a duniya, yayin da ya zama mutum na farko a duniya da ya samu mabiya sama da miliyan dubu dari biyu a shafinsa na Instagram

- Cristiano wanda yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Juventus ya samu wannan nasara ne a farkon wannan shekara ta 2020

- Dan wasan wanda yake dan asalin kasar Portuagal ya shigo wannan shekara da kafar dama

Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa na Juventus kuma dan asalin kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya bar tarihi a dandalin sada zumunta na Instagram, bayan ya samu mabiya miliyan 200.

Shekarar 2020 bisa dukkan alamu shekarar sa’a ce ga fitaccen dan wasan, bayan ya sake samun wannan gagarumar nasara a rayuwa.

Wannan dai ita ce nasara ta farko da ya samu a shekarar 2019, inda ta faru a ranar 29 ga watan Janairu, 2020.

Cristiano ya bar tarihi a duniya, yayin da ya zama mutum na farko da yafi kowa mabiya a Instagram a duniya
Cristiano ya bar tarihi a duniya, yayin da ya zama mutum na farko da yafi kowa mabiya a Instagram a duniya
Asali: UGC

Mai biye mishi ita ce Ariana Grande, wacce ke da mabiya miliyan 172. Daga ita kuma sai fitaccen dan wasan kokawar nan kuma jarumin wasan fim na kasar Amurka, wato Dwayne Johnson wanda aka fi sani da The Rock, inda yake da mabiya miliyan 169.

KU KARANTA: Kare da akuya sun shiga takarar neman sarauta a birnin Fair Heaven na kasar Amurka

Ga jerin manyan mutanen da suke da mabiya mafi yawa a duniya a kasa:

1. Instagram (@Instagram): 330 million followers.

2. Cristiano Ronaldo (@cristiano): 200 million followers.

3. Ariana Grande (@arianagrande): 172 million followers.

4. Dwayne Johnson (@therock): 169 million followers.

5. Selena Gómez (@selenagomez): 166 million followers.

6. Kylie Jenner (@kyliejenner): 158 million followers.

7. Kim Kardashian (@kimkardashian): 157 million followers.

8. Lionel Messi (@leomessi): 141 million followers.

9. Beyoncé (@beyonce): 138 million followers.

10. Neymar (@neymarjr): 131 million followers.

Hakan na nuni da cewa dan wasan koda a yanzu zai daina taka leda a duniya, to wannan nasara da ya samu a Instagram ta isa ta sanya ya dinga samun makudan kudade a kowacce rana.

Fannin sada zumunta dai ya zama wajen samun kudi ga mutane da yawa a duniya, inda wasu ke kashe makudan kudade domin fara sana'a a kafafen sada zumunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng