Kyawun surar Ronaldo da tsawonshi ya sanya naji babu wani wanda nake so a duniya kamar shi - Georgina Rodriguez

Kyawun surar Ronaldo da tsawonshi ya sanya naji babu wani wanda nake so a duniya kamar shi - Georgina Rodriguez

- Georgina Rodriguez ta bayyana cewa ta fara son Ronaldo ne tun ganin shi da tayi na farko saboda tsawon shi, kyau da kuma kirar jikin shi

- Ta hadu da Ronaldo ne a wani shagon siyar da kayayyakin kamfanin Gucci a Real Madrid inda take tsaron shagon

- Dukkansu sun fada matsananciyar kaunar juna tare da goyon bayan juna ta yadda zasu cimma burikansu a rayuwa

Georgina Rodriguez ta bayyana yadda shahararren dan kwallon kafa Ronaldo ya sace zuciyarta baki daya. Wannan ya bayyana ne bayan da ake rade-radin cewa masoyan sun yi aure.

A lokacin da yake wasa da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Ronaldo ya hadu da budurwar mai shekaru 26 wacce ke aiki a babban shagon siyar da kayayyakin kamfanin Gucci da ke kasar Spain.

Kyawun surar Ronaldo da tsawonshi ya sanya naji babu wani wanda nake so a duniya kamar shi - Georgina Rodriguez
Kyawun surar Ronaldo da tsawonshi ya sanya naji babu wani wanda nake so a duniya kamar shi - Georgina Rodriguez
Asali: Getty Images

Sun kai shekaru hudu suna soyayya kuma sun haifa diya daya mai suna Alana Martina. Masoyiyar Ronaldo din ce ke rike da sauran 'ya'ya uku nashi.

A yayin da take zantawa da wata mujallar Italia mai suna Grazia, Georgina ta yi bayanin yadda tayi ta kokarin sabawa da sanayyar da aka yi wa masoyinta. Ta ce kallon farko ta fara son shi saboda tsawon shi, kirar shi da kuma kyan shi.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: Bature ya yi shiga irinta bakar fata yaje ya yi fashi a banki

"Abinda ya ja hankalina shine tsawon shi, kirar jikin shi da kuma kyan shi," mahaifiyar yarinya daya ta sanar.

"Jikina rawa ya fara amma kuma ina da matukar kunya ko da kuwa a wajen wanda na fara so ne a take daga ganin shi. Daga yadda ya ke min, kula dani da kuma kaunata yasa na ci gaba da son shi."

A koda yaushe Cristiano Ronaldo na bayyana sa'a da yayi a kan samun mahaifiya da kuma mata duk a Georgina.

A cikin kwanakin nan ne ya nuna tsananin kaunar da yake wa Georgina a wani bidiyon shagalin ranar zagayowar haihuwarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel