Ronaldo ne mafi kyawun ‘Dan wasan gaban da Messi ya taba gani

Ronaldo ne mafi kyawun ‘Dan wasan gaban da Messi ya taba gani

Tauraron Duniya, Lionel Messi, ya yi hira da TYC Sports jim kadan bayan ya samu sauki ya dawo buga wasa. Idan ba ku manta ba kwanakin baya rauni ya hana ‘dan kwallon buga wasanni.

An yi wa ‘Dan wasan Duniyan tambayoyi da-dama, ya na bada amsoshinsa. Messi ya tabbatar da cewa bai da niyyar barin Barcelona. Ga kadan daga cikin tambayoyin da aka yi wa Tauraron.

VAR

“Ina son fasahar VAR idan aka yi amfani da ita da kyau. Abin da ba na so shi ne an kawo ta ne domin ta rika warwera shakku, amma har yanzu ba ta yin wannan.

Kwallon farko

“Kafin kwallon ya dura kasa, sai na dauke daga hannun ‘dan baya, na mikawa Ronaldinho, na kuma jira, sai ya cako mani ita, ni kuma na aske gola. Na ci irin ta a baya, amma aka kashe…”

KU KARANTA: Hujjoji sun fara nuna akwai alamun gaskiya a zargin da ake yi wa Ronaldo

Abokan wasa

"Rondaldinho ya taimaki mani sosai a lokacin da na zo ina ‘dan shekara 16-17. Ganin Taurari irinsu ya taimaka mani…Na yi shekaru biyar ina wasa da Luis Suarez duk bayan kwana uku. Mun saba da juna. Mu na da ‘ya ‘ya sa’annin juna. Kullum tare da mu ke rayuwa. Abin sai gaba yake yi.”

‘Dan kwallon gaban da ya fi kowa

"Ronaldo [Nazario] ‘Dan Baiwa ne. A duk ‘yan wasan gaban da na gani a Duniya, ya fi kowa. Ronaldo abin mamaki ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel