Cristiano Ronaldo ne ‘Dan kwallon da ya fi kowa arziki; ya ba $460m baya
Cristiano Ronaldo bai kai Abokin gabansa Lionel Messi yawan Ballon D’or ba, amma kuma ‘Dan wasan na Juventus ya sha gaban Messi idan aka zo maganar dukiya.
‘Yan wasan biyu su ne manyan Taurarin da ake ji da su a Duniya. Tsakaninsu kawai an samu Ballon D’or na babban ‘Dan wasan Duniya sau 11 daga 2008 zuwa yau.
Bincike ya nuna cewa Cristiano Ronaldo ya sha gaban kowane ‘Dan wasa kwallon kafa a maganar kudi. Albashin da ya ke karba a Italiya ya kai Dala miliyan 34.
Hakan na nufin duk shekara, Ronaldo na tashi abin da ya kai akalla fam miliyan €31. Amma kuma bayan hakan akwai wasu hanyoyin da Tauraron ya ke samun kudi.
Shi kuwa Lionel Messi wanda ya ke bugawa Barcelona ya na tashi da fam €40 a shekara. Kwantiragin Messi zai kare ne a cikin shekara mai zuwa watau 2021.
KU KARANTA: Tsohon Koci Audu Pele ya rasu
Duk da wannan. Ronaldo ya na bayan LeBron James ne kawai wajen samun kudi da kamfanin Nike. Ana hasashen Ronaldo ya tada kai da akalla dala miliyan 460.
A kudin Najeriya wannan kudi da Ronaldo ya mallaka sun haura Naira biliyan 150. Daga cikin hanyoyin da Ronaldo ya ke samun kudi akwai shafinsa na Instagram.
Haka zalika kamfanin tsohon ‘Dan wasan na Real Madrid watau CR7 ya na jawo masa kudi a Mahaifarsa Portugal, Sifen, Italiya da wasu manyan Biranen Duniya.
Shi kuwa Messi, ana hangen cewa ya mallaki Dala miliyan 400 ne a halin yanzu. Da miliyan £309 a asusunsa, babu wanda ya kai Lionel Messi samun kudi a kasar Sifen.
A kowane mako, Messi ya na karbar £500,000 a Barcelona. Kafin wannan kwantiragi da ya sa wa hannu a shekarar 2017, Ana biyan ‘Dan wasan gaban fam £336,000 ne.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng