Ballon D’or: Cikakken Jerin Taurarin ‘Yan wasan Duniya na shekarar bana

Ballon D’or: Cikakken Jerin Taurarin ‘Yan wasan Duniya na shekarar bana

A daren jiya, 2 ga Watan Disamban 2019, Lionel Messi ya kafa tarihin zama ‘dan kwallon da ya taba lashe kyautar Ballon D’or sau shida a tarihi. Wannan ya sa ya sha gaban Cristiano Ronaldo.

Mun kawo maku cikakken jerin yadda zaben Gwarazan na wannan shekara ya kasance. Van Dijk shi ne ya zo na biyu a wannan shekara, yayin da Cristiano Ronaldo ya cike ragowar sahun farkon.

1. Lionel Messi (Barcelona)

2. Virgil van Dijk (Liverpool)

3. Cristiano Ronaldo (Juventus)

4. Sadio Mane (Liverpool)

5. Mohamed Salah (Liverpool)

Manyan ‘Yan wasan Liverpool; Sadio Mane, Mohammed Salah da Alisson Becker su na matakin farko. Kylian Mbappe ne kadai ‘Dan wasa daga Ligue I da ya shiga cikin sahun ashirin na farko.

6. Kylian Mbappe (PSG)

7. Alisson Becker (Liverpool)

8. Robert Lewandowski (Bayern Munich)

9. Bernardo Silva (Man City)

10. Riyad Mahrez (Man City)

KU KARANTA: Messi ya tafi da Ballon D'or na 6 a tarihin kwallon kafa

Akwai ‘Yan wasan Liverpool 7 a jerin na mutum 30, Manchester City ta na da wakilcin ‘Yan wasa 5. Tottenham ta tashi da 2, Arsenal ta samu guda. ‘Yan wasan Firimiya ne su ka cika jeringiyar.

11. Frenkie de Jong (Barcelona)

12. Raheem Sterling (Man City)

13. Eden Hazard (Real Madrid)

14. Kevin De Bruyne (Man City)

15. Matthijs de Ligt (Juventus)

Sai kuma jerin na 16-20

16. Sergio Aguero (Man City)

17. Roberto Firmino (Liverpool)

18. Antoine Griezmann (Barcelona)

19. Trent Alexander-Arnold (Liverpool)

20. Pierre-Emerick Aubameyang (Arsenal) da Dusan Tadic (Ajax)

21. Kunnen-doki

Real Madrid ta samu ‘yan wasa biyu ne rak a jerin kamar dai Juventus da Ajax. Bayern Munchen ta tashi da ‘dan kwallo guda, haka zalika Atletico Madrid. ‘Dan wasan Napoli guda ya samu shiga.

22. Heung-Min Son (Tottenham)

23. Hugo Lloris (Tottenham)

24. Marc-Andre Ter Stegen (Barcelona)

25. Kalidou Koulibaly (Napoli)

26. Karim Benzema (Real Madrid) and Georginio Wijnaldum (Liverpool)

27. Kunnen-doki

28. Donny van de Beek (Ajax) da Joao Felix (Atletico Madrid) da Marquinhos (PSG)

An sake samun kunnen-doki a ragowar na 28 zuwa 30.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng