Cristiano Ronaldo ne Gwarzon ‘Dan kwallon Seria A na shekarar 2019
Tauraron ‘Dan wasan gaban kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar babban ‘dan kwallon kafa na kasar Italiya bayan ya rasa Ballon D’or na Duniya a hannun Lionel Messi jiya.
A Ranar Litinin, 2 ga Watan Disamban 2019, Lionel Messi ya kerewa Cristiano Ronaldo, ya zama ‘dan kwallo na farko da ya lashe Ballon D’or sau shida. Ba a taba yin wannan a tarihin wasan ba.
Cristiano Ronaldo wanda ya zo na uku a Duniya a wannan shekarar, bayan Lionel Messi da Virgil Van Dijk ya yi nasara a gida, inda ya samu kyautar babban ‘dan wasan Gasar Seria A na bana.
A lokacin da ake bikin Ballon D’or a babban birnin Faransa na Faris, Ronaldo ya na kasar Italiya. Shi ma Ronaldo ya gama wannan shekarar a matsayin Gwarzon ‘dan kwallon kasar Italiya.
KU KARANTA: Messi na 1, Van Dijk na 2 sai Ronaldo na 3 a zaben Ballon D'or
Bayan ya karbi wannan kyauta, Jaridar Marca ta rahoto Ronaldo ya na mai cewa: “Ina alfaharin zama babban ‘Dan wasa a Seria A. Ina godewa Abokan wasa na da duk wadanda su ka zabe ni.”
‘Dan wasan gaban ya kuma tabbatar da cewa zai cigaba da buga wasa a kungiyarsa ta Juventus akalla har zuwa shekara mai zuwa. Ya ce: “Yanzu zan dage in cigaba da wasa a nan har badi.”
Haka zalika an sa Ronaldo a cikin Tawagar ‘yan wasan shekarar 2019. A cikin jeringiyar ‘Yan wasa 11 da su ka yi fice a bana akwai Ronaldo tare da Fabio Quagliarella da Duvan Zapata a gaba.
Sauran Taurarin ‘Yan wasan na bana su ne: Samir Handanovic, Joao Cancelo, Giorgio Chiellini Kalidou Koulibaly, Aleksandar Kolarov, Miralem Pjanic, Nicolo Barella, sai kuma Josip Ilicic.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng