An fara rade-radin Lionel Messi zai zama Gwarzon ‘Dan kwallon Duniya
Kawo yanzu, rade-radi na yawo cewa Lionel Messi ne zai zama Gwarzon ‘Dan wasan kwallon kafa na shekarar bana. Idan wannan ta tabbata, Lionel Messi zai karbi Ballon D’or dinsa na shida.
Jaridun waje sun bayyana cewa an samu labarin wadanda za su lashe kyaututtukan wannan shekara kafin a kai ga lokacin sanarwa. Sai dai babu sahihancin wadannan sunaye da ke yawo.
Kamar yadda wannan jeri da ya fito a boye ya bayyana, ‘Dan wasan gaban na kasar Argentina zai doke Virgil van Dijk na Liverpool wanda ya yi nasarar dukar gasar kofin Nahiyar Turai a bana.
Messi ya ba ‘Dan bayan na Liverpool ratar maki fiye da 60. Wanda zai zo na uku a jerin shi ne Mohammed Salah. Takwaransa ‘Dan wasan Liverpool, Sadio Mane yana biye a mataki na biyar.
KU KARANTA: An bayyana albashin Mourinho bayan ya karbi aikin Tottenham
Har ila yau idan wannan labari ya tabbata, za a tsinci Cristiano Ronaldo ne a na hudu wannan shekarar. Wannan ne karon farko da za a samu ‘dan wasan bai cikin sahu biyun farko tun 2011.
Ronaldo wanda ya koma taka leda a Juventus bayan barin Real Madrid a bara, ya dauki tsawon shekaru a cikin sahun farko. ‘Dan wasan na kasar Portugal ya lashe kyautar Ballon D’or sau biyar.
‘Yan wasan Liverpool za su ci kasuwa a shekarar bana, muddin jerin da ya fito ya zama gaskiya. Mai tsaron ragar Liverpool watau Alisson Becker ne ake tsammani zai shiga na shida a jeringiyar.
A karashen wannan jeringiyar na ‘yan wasa goma, Kylian Mbappe ne ya zo na bakwai. Frenkie de Jong da Matthijs de Ligt da kuma Eden Hazard ne su ka rufe sahun goman farko a shekarar 2019.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng