AC Milan: Daniel Maldini ya buga wasansa na farko a Seria A
‘Dan wasa Daniel Maldini, wanda ‘Da ne wajen Paolo Maldini, kuma Jikan Cesare Maldini, ya bugawa AC Milan kwallonsa na farko a tarihinsa.
A karshen makon da ya wuce ne Daniel Maldini ya bugawa AC Milan kwallo a matsayin babban ‘Dan wasa a karawarsu da kungiyar Hellas Verona.
Daniel Maldini ya sha ban-ban da tsofaffinsa wadanda su ka kasance ‘Yan wasan baya. Matashin ‘Dan kwallon ya na buga kowace lamba a saman fili.
Maldini ya kan buga a matsayin ‘Dan wasan gaba ta gefe ko kuma ya tsaya a bayan mai cin kwallo. ‘Dan kwallon ya na da shekaru 18 ne yanzu.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ‘Dan wasan gaban ya burge ‘Yan kallo a jerin wasannin da aka buga kafin a soma gasar kakar wannan shekarar.
KU KARANTA: Ronaldo ya maimaita abin da Trezequet ya yi a shekarar 2005
Bayan nuna gwanintarsa a wasannin sharan fagen sabon kaka ne aka fara tunanin amfani da Daniel Maldini a manyan wasannin da AC za su buga.
Bayan ganin wasan ‘Dan da ya haifa, Paulo Maldini ya fito ya na cewa: “Shi ‘Dan kwallo ne mai gyara wasa, kuma mai jefa kwallo a raga, kuma 10.”
Mahaifin ‘Dan kwallon da ke tasowa ya yabawa irin baiwar da Ubangiji ya yi masa na wasa da kwallo, abin da ba a taba samu a gidan Maldini ba.
“Shi ma kusan iri na ne wajen iya amfani da kafar dama da ta hagu. Ya dauko baiwa ta da ta mahaifi na.” Inji tsohon ‘Dan wasa Paolo Maldini.
“Daga yadda ya ke tafiya a lokacin ya na karamin yaro, ya yi kama da yadda wasu su ka rika ganin kamannin Mahaifi na a jiki na. Gado ne.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng